An haifi Joshua Ogunwole a garin Ibadan a ranar 23, ga watan Yuli 1967. Shi masanin kimiyyar ƙasa ne a Najeriya wanda a halin yanzu yake aiki a matsayin mataimakin shugaba na 4, na jami'ar Bowen.[1]

Joshua Olalekan Ogunwole
Rayuwa
Haihuwa Jahar Ibadan, 23 ga Yuli, 1967 (57 shekaru)
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a scientist (en) Fassara

Ilimi da aikiaiki.

gyara sashe

Ogunwole ya yi digirinsa na farko da na biyu da na uku a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A tsakanin shekarar 1990-1992, ya yi aiki a matsayin manaja na gonar Yula, Kaduna.[2]

Ogunwole ya koyar a sashen samar da amfanin gona da kariya na jami'ar tarayya dake Dutsin-Ma a tsakanin watan Dec 2013 - Maris 2016, kuma ya zama darakta na ci gaban jami'a da haɗin gwiwa.[3]

Shi Farfesa ne a fannin ilimin kimiyyar ƙasa, Sashen Kimiyyar Ƙasa da Gudanar da albarkatun ƙasa, a Jami'ar Tarayya dake Oye-Ekiti, har zuwa lokacin da aka naɗa shi a matsayin mataimakin shugaban jami'ar Bowen.[4]

Hanyoyin sadarwa da kyaututtuka.

gyara sashe

A cikin shekarar 2004, Joshua Ogunwole ya sami lambar yabo ta bincike don aikin noma mai ɗorewa, daga gidauniyar Schweisfurth da tallafawa Afirka ta ƙasa da ƙasa ta Jamus.[5]


A shekarar 2012, a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ya samu nasarar shirya taron karawa juna sani na ƙasa da ƙasa kan tsarin tafiyar da jikin ƙasa a yammacin Afirka.[6]


An shigar da Ogunwole a Kwalejin Nazarin Associates na Jami'ar Majalisar Ɗinkin Duniya-Cibiyar Albarkatun Ƙasa na Afirka a cikin shekarar 2015. Shi memba ne na al'ummar kimiyyar ƙasa a Najeriya.[7]

Ayyuka sun haɗa da:

Takardun bincike da muƙaloli.

gyara sashe

Joshua Ogunwole ya rubuta fiye da takarda bincike guda 60, da muƙala, sanannu daga cikinsu akwai:

Manazarta.

gyara sashe
  1. "Absence Of Link Between Varsities' Research, Industries Stalling Nigeria's Development — Ogunwole – Bowen" (in Turanci). Retrieved 2019-12-19.
  2. "Joshua Ogunwole Archives". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2019-12-19. Retrieved 2019-12-19.
  3. "Bowen University appoints Ogunwole as new vice-chancellor". Punch Newspapers (in Turanci). 14 August 2018. Retrieved 2019-12-19.
  4. https://www.pressreader.com/nigeria/the-punch/20191119/282278142167602. Retrieved 2019-12-19 – via PressReader. Missing or empty |title= (help)
  5. "Joshua O. Ogunwole - Google Scholar Citations". scholar.google.com. Retrieved 2019-12-19.
  6. "Absence of link between varsities' research, industries stalling Nigeria's development — Prof Ogunwole, VC, Bowen varsity". Punch Newspapers (in Turanci). 14 July 2019. Retrieved 2019-12-19.
  7. "Professor Joshua Ogunwole Assumes Duty as the Vice Chancellor of Bowen University, Iwo". SSSN (in Turanci). 2018-08-03. Archived from the original on 2019-12-19. Retrieved 2019-12-19.