Jibril Aminu

Dan Siyasa a Najeriya

Jibril Muhammad Aminu (An haife shi a watan Agusta, shekara ta 1939). Farfesa ne a fannin ilimin zuciya.[1] ya kasance Jakadan Najeriya a Amurka daga shekarar 1999 zuwa 2003. Kuma an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a jihar Adamawa, Najeriya, inda ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayu shekara ta 2003. Dan jam'iyyar PDP ne.[2]

Jibril Aminu
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 2003 - Mayu 2011
Abubakar Girei - Bello Mohammed Tukur
District: Adamawa Central
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

1999 - 2003
ambassador (en) Fassara


mataimakin shugaban jami'a


vice dean (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Jihar Adamawa, 12 ga Augusta, 1939 (85 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Kwalejin Barewa
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Mai wanzar da zaman lafiya, cardiologist (en) Fassara da Farfesa
Employers Howard University (en) Fassara
Jami'ar Maiduguri
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
Jibril Aminu

Haihuwa da aikin ilimi

gyara sashe

An haifi Aminu a watan Agusta na shekarar 1939. Ya yi karatun likitanci, inda ya samu digiri na MBBS daga Jami’ar Ibadan a shekarar 1965, sannan ya sami digiri na uku a fannin likitanci daga Royal Post-Graduate Medical School dake Landan a shekarar 1972.

An naɗa shi Fellow of the Nigerian Academy of Science in 1972, Fellow of the Royal College of Physicians, London a shekarar 1980 da Fellow of West African College of Physicians shi ma a shekarar 1980.

An maishe shi Babban Jami'in Kwalejin Kiwon Lafiya ta Najeriya a shekarar 2004.[2]

Aminu ya kasance mai ba da shawara a fannin likitanci, Babban Malami kuma Babban Dean, Nazarin Clinical a Makarantar Kiwon Lafiya ta Jami'ar Ibadan daga shekarar 1973 zuwa 1975 kuma Babban Sakatare na Hukumar Kula da Jami'o'i ta ƙasa daga shekarar 1975 zuwa 1979.

Aminu ya kasance Farfesan Likita a Jami'ar Howard da ke Washington DC (1979-1980) kuma Mataimakin Shugaban Jami'ar Maiduguri daga shekarar 1980-1985. Ya kuma taɓa zama Farfesa a fannin likitanci a Jami'ar Maiduguri daga 1979 zuwa 1995.[2]

Sana'ar siyasa

gyara sashe

Aminu ya riƙe muƙamin ministan ilimi na tarayya sannan kuma ya riƙe ministan man fetur da ma'adinai na tarayya daga shekarar 1989 zuwa 1992.

Lokacin da yayi ministan man fetur ya kasance shugaban ƙungiyar masu samar da man fetur ta Afrika (1991) kuma shugaban ƙungiyar OPEC (1991-1992).

An zaɓe shi a matsayin wakilin Majalisar Tsarin Mulki na Kasa (1994-1995).

Daga shekarar 1999 zuwa 2003, Aminu ya kasance jakadan Najeriya a ƙasar Amurka.[2]

An zaɓi Aminu a matsayin ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a shekarar 2003 sannan aka sake zaɓenshi a shekarar 2007. A matsayin Sanata Aminu an naɗa shi a kwamitocin harkokin ƙasashen waje, ilimi, sojojin sama da lafiya.[2] A wani nazari na tsakiyar wa’adi da Sanatoci suka yi a watan Mayun 2009, Thisday ya ce bai ɗauki nauyin wani ƙudiri ba, amma ya bayar da gudunmawa wajen muhawara kan wasu ƙudirori. Ya tafiyar da Kwamitin Harkokin Waje da kyau, kuma ya himmantu sosai ga ayyukan Kwamitin Ilimi.[3]

A ranar 2 ga watan Janairu na shekarar 2010, Ooni na Ife, Oba Sijuwade, ya naɗa Aminu "Bobaselu of The Source".[1]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Jibril Aminu ya yi aure sau biyu. Matarsa a yanzu ita ce Hajiya Fatima Bukar Mulima wadda ta haifa masa ƴaƴa guda uku (3). Matarsa da ya saki ita ce Hajiya Ladi Ahmed, wadda ta haifa masa ƴaƴa shidda (6). Ƴaƴansa Bashiru Aminu da Murtala Muhammad Aminu masana tattalin arziki ne kuma ƴan kasuwa ne yayin da ƴaƴansa mata kuma ke aiki a matsayin lauyoyi (Nana Aminu) da likitan haƙori ( Aminu Bello).[4]

Manazarta

gyara sashe