Ja'afar Abubakar Magaji ɗan siyasan Najeriya ne. A yanzu haka ya zama ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Mubi ta Arewa/Mubi ta kudu/Maiha a majalisar wakilai. [1] [2]

Ja'afar Abubakar Magaji
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
Abdulrahman Shuaibu Abubakar
District: Maiha/Mubi North/Mubi South
Rayuwa
Haihuwa Jihar Adamawa, 4 Oktoba 1980 (44 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Employers gwmanatin najeriya
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Ja'afar Abubakar Magaji a ranar 4 ga watan Oktoba 1980 kuma ya yi karatun digiri na biyu (BSc). a fannin Gudanar da Kasuwanci. [1]

Aikin siyasa

gyara sashe

A zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC na mazaɓar Mubi ta Arewa/Mubi ta Kudu/Maiha a shekarar 2022, Ja’afar ne ya lashe zaɓen yayin da ya kayar da wasu ‘yan takara huɗu a zaɓen. [3] A matsayin tallafi da karfafawa, Jafar ya samarwa al’ummar mazaɓar sa taki tirela guda uku, daruruwan magungunan kashe kwari da na ciyawa, da kuma kayayyakin noma. [4]

Kalubale na shari'a da nasara

gyara sashe

A zaɓen shekara ta 2023 na majalisar wakilai ta ƙasa, wata kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta bayyana Jaafar Magaji ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen mazaɓar tare da umurci INEC ta ba shi takardar shaidar cin zaɓe., yayin da ya kori Jingi Rufa'i na jam'iyyar PDP. [5]

Ja'afar Abubakar Magaji musulmi ne.

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "10th National Assembly Members - Voter - Validating the Office of the Electorate on Representation". orderpaper.ng. Retrieved 2024-12-11. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-11.
  3. Ochetenwu, Jim (2022-07-25). "Adamawa: Aspirants sue INEC over alleged insignificant votes in Mubi/Maiha APC Reps primary". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-12-11.
  4. Team, Editorial (2024-09-01). "Adamawa constituents Hail Jafar as Hero of Agricultural Development - TG News" (in Turanci). Retrieved 2024-12-11.
  5. BusinessDay (2023-10-25). "Zango, Magaji sworn in as new House of Reps members". Businessday NG (in Turanci). Retrieved 2024-12-11.