Mubi birni ne, da ke a gundumar Arewa a Jihar Adamawa, dake arewa maso gabashin Najeriya. Mubi ta rabu zuwa kashi biyu.

Mubi


Wuri
Map
 10°15′37″N 13°15′38″E / 10.2604°N 13.2606°E / 10.2604; 13.2606
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Adamawa
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Jami ar mubi
Mibi gidan sarki
Jami ar mubi

Mubi ta arewa da Mubi kudu

Manyan kabilan garin sun hada da Fali, Gude, Kamwe, Margi da Mundang (Godo-godo).

 
jami'ar jaha ta adamawa

Mubi tana da manyan cibiyoyin koyo guda uku: Federal Polytechnic, Mubi, [1] College of Health Technology (Mubi Campus), da Jami'ar Jihar Adamawa, Mubi. [2]

Boko Haram ta kwace garin

gyara sashe

Wasu kafafen yada labarai sun bada sanarwa cewa an canzawa birnin suna zuwa Madinatul Islam, ma'ana birnin Musulunci da kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin cewa a watan Oktoban 2014 lokacin da suka kwace garin da ke karkashin ikonsu.[ana buƙatar hujja]

A watan Nuwamban shekarar 2014 ne sojojin Najeriya suka kwato garin Mubi daga hannun 'yan Boko Haram. Gwamnan jihar Adamawa Barr. Bala Ngilari ya ce dakarun gwamnati sun kwato garin daga hannun 'yan Boko Haram. Wasu rahotanni sun kuma ce 'yan Boko Haram sun janye daga garin ne bayan sun wawashe kayayyaki da kudaden jama'a zuwa maboyarsu daga garin, amma ba sakamakon fadan kai tsayeya ba. Sai dai shugaban ma’aikata na Bala Ngilari, Chibudo Babbi ya shaidawa Sashen Hausa na BBC cewa sojoji sun fatattaki ragowar kungiyar daga Mubi.[3]

Kashe-kashe

gyara sashe

Wani harin ta'addanci da aka kai a ranar 2 ga watan Oktoban 2012 lokacin da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka shiga garin da misalin karfe 10 na dare suka kashe mutane da dama. Galibin wadanda abin ya shafa dai dalibai ne daga cibiyoyin ilimi guda uku ( Federal Polytechnic Mubi, School Of Health Technology da Jami'ar Jihar Adamawa ) dake garin. An bayyana adadin wadanda suka mutu a farko zuwa 25, amma an ce adadin ya kusan kusan 45.[4]

An kai harin bam a Mubi a ranar 1 ga watan Yunin shekarata 2014.

A ranar 21 ga watan Nuwamban 2017, wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci a lokacin sallar asuba ya yi sanadiyar mutuwar mutane 25-50. Boko Haram ne ake zargi ta aikata laifin.

 
wuraren da akayi gudun hijira lokacin boka haram

An kai harin kunar bakin wake a wani masallaci da kasuwa a garin Mubi a shekarar 2018.

Tsarin kasafin yanayi na Köppen-Geiger yana rarraba yanayin garin azaman Tropical wet and dry climate (Aw).

Climate data for Mubi, Adamawa
Watan Janairu Fabrairu Maris Afrilu Mayu Yuni Yuli Ogusta Satumba Oktoba Nuwamba Disamba Shekara
Average high °C (°F) 32
(90)
33.9
(93.0)
36.4
(97.5)
36.7
(98.1)
33.9
(93.0)
30.9
(87.6)
28.8
(83.8)
27.8
(82.0)
29
(84)
32
(90)
33.5
(92.3)
32
(90)
32.2
(90.1)
Daily mean °C (°F) 23.5
(74.3)
25.6
(78.1)
28.3
(82.9)
29.3
(84.7)
27.5
(81.5)
25.4
(77.7)
24
(75)
23.4
(74.1)
24
(75)
25.2
(77.4)
25.2
(77.4)
23.4
(74.1)
25.4
(77.7)
Average low °C (°F) 15
(59)
17.3
(63.1)
20.3
(68.5)
22
(72)
21.2
(70.2)
19.9
(67.8)
19.3
(66.7)
19.1
(66.4)
19
(66)
18.5
(65.3)
16.9
(62.4)
14.9
(58.8)
18.6
(65.5)
Average precipitation mm (inches) 0
(0)
0
(0)
3
(0.1)
30
(1.2)
98
(3.9)
135
(5.3)
202
(8.0)
258
(10.2)
164
(6.5)
43
(1.7)
2
(0.1)
0
(0)
935
(37)
Source: Climate-Data.org (altitude: 572m)[5]

Kasuwar shanu

gyara sashe

Mubi gidan shahararriyar kasuwar shanu ta kasa da kasa wadda aka fi sani da kasuwan shanu ko kuma Kasuwan tike dake tsakiyar garin, kwastomomi masu yawan gaske ne suke siyan shanu da tumaki musamman daga arewa maso gabashin Najeriya ana rarraba su zuwa sassa daban-daban na kudancin kasar Najeriya ta tireloli da manyan motoci.[6]

Sanannen mazauna

gyara sashe

Mubi gida ce ga fitattun yan Najeriya da suka hada da:

  • Iya Abubakar (Prof of Mathematics)
  • Alex Badeh (Tsohon Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya)
  • Bindow Umar Jibrilla (Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa)
  • Ibrahim Lamorde (Tsohon Shugaban EFCC)

Manazarta

gyara sashe
  1. "The Federal Polytechnic Mubi". Archived from the original on 2022-01-20. Retrieved 2022-02-06.
  2. History of Adamawa State University
  3. "Nigeria army 'retakes Mubi from Boko Haram'". BBC News. Retrieved 13 November 2014.
  4. "Nigeria: Gunmen Kill 46 Students in Mubi, Africa: Allafrica.com, 2012, retrieved 4 October 2012
  5. "Temperature, Climograph, Climate table for Mubi". Climate-Data.org. Retrieved 2018-05-02.
  6. "Kashuwar Sanu (cattle market) in the town of Mubi – OSUN DEFENDER". Archived from the original on 2016-03-04.

wuri 10°16′N 13°16′E / 10.267°N 13.267°E / 10.267; 13.267