Ibiyinka A. Fuwape (an haife ta a ranar 18 ga watan Disamba 1962) Malama ce 'yar ƙasar Najeriya, farfesa a fannin kimiyyar lissafi kuma babbar mataimakiyar shugaban jami'ar Michael da Cecilia Ibru na biyu,[1] jami'a ce mai zaman kanta a Najeriya.

Ibiyinka A. Fuwape
Rayuwa
Haihuwa jahar Lagos, 18 Disamba 1962 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Methodist Girls' High School (en) Fassara
Jami'ar Ibadan
Jami'ar Ibadan
Matakin karatu Digiri a kimiyya
Master of Science (en) Fassara
Doctor of Philosophy (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami, physicist (en) Fassara, university teacher (en) Fassara, mataimakin shugaban jami'a da malamin jami'a

Rayuwar farko

gyara sashe

An haifi Ibiyinka Fuwape a jihar Legas a ranar 8 ga watan Disamba, 1962 'ya ce ga dangin David Ademokun.[2] Ta fara karatun ta ne a Reagan Memorial Baptist Girls Primary School, Yaba, Legas.[3] Ta wuce makarantar sakandaren ‘yan mata ta Methodist inda ta samu takardar shedar karatun ta na yau da kullun, daga baya ta samu takardar shedar sakandare daga shekarun 1979 zuwa 1981 a Queen’s College Yaba. Ta kammala karatun digiri a jami'ar Ibadan da digiri na farko a fannin kimiyyar lissafi (B.Sc.).[4] Ta sami Master of Science (M.Sc.) a cikin shekarar 1986, da Dakta ta Falsafa (PhD) a fannin ilimin kimiyyar lissafi.[3]

Ibiyinka ta fara aiki a matsayin mataimakiyar malami a shekarar 1989 a Jami'ar Fasaha ta Tarayya, Akure,[5] kuma an kara mata girma zuwa Farfesa a cikin watan Oktoba 2003. Ta yi aiki a matsayin Shugabar Sashen riƙo kuma Shugabar Sashen Physics na tsawon shekaru tara. Ta kuma yi aiki a matsayin Dean, a sashen Makarantar Kimiyya daga shekarun 2011 zuwa 2015. Ta kasance memba a Majalisar Dattawa ta Jami'ar daga shekarun 2003 zuwa 2017, kuma ta kasance shugabar Majalisar Dattawa a lokacin zaman karatun 2014/2015. Ta lashe kyautar Dean of the Year a shekara ta 2012.

Ibiyinka Fuwape Malama ce mai ziyara a Jami'ar Ohio Athens, Ohio, Amurka (Amurka) daga shekarun 2007-2009. Ta wallafa takardu da yawa a cikin manyan mujallu na gida da waje. [1]

Ta kasance mataimakiyar memba na Cibiyar Abdus Salam da ilimin kimiyyar ka'idar a Trieste, Italiya, daga shekarun 1996 zuwa 2002.[6] Binciken ta a Cibiyar yana mayar da hankali ne kan tsarin da ba na layi ba.[7] Ta zama Jagorar Ƙungiyar International Union of Pure and Applied Physics working group for women a cikin shekarar 2002 kuma har yanzu tana da hannu a ayyukan wannan rukuni. A cikin shekarar 2006 ta zama Schlumberger Fellow, a cikin shirin da Gidauniyar Schlumberger ta kafa don tallafawa ilimin kimiyya da fasaha.[8]

Binciken da ta yi a halin yanzu game da hargitsin yanayi na ƙananan yanayi.[9]

Girmamawa da kyaututtuka

gyara sashe

A cikin shekarar 2018, Fuwape ta kasance mai karɓar lacca na Marshak Society na Physical Society. Jawabin nata a taron kungiyar ya shafi batun 'Mata a fannin Physics a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka kudu da hamadar Sahara: Ci gaba da kalubale'.[10] Ita ce ta samu lambar yabo ta African Union Kwame Nkrumah Regional Award for Scientific Excellence, a shekarar 2020.[11]

An naɗa ta a matsayin Fellow of the American Physical Society a cikin shekarar 2022 "tsawon shekarun da suka gabata na jagoranci a ci gaban mata a fannin kimiyyar lissafi a Najeriya da Afirka, tare da manyan gudummawar bincike don magance matsalolin sauyin yanayi, noma, da kuɗi a fannin ilimin kimiyyar lissafi al'umma, ta yadda za su amfana da ci gaban tattalin arziki a Afirka".[12]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Ta auri Joseph Fuwape, mataimakin shugaban jami'ar fasaha ta tarayya Akure a halin yanzu.[13]

Manazarta

gyara sashe
  1. Nigeria, Guardian (2021-03-24). "Ibru varsity gets NUC's approval for 13 new courses, holds joint matriculation". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2023-06-24. Retrieved 2023-06-24.
  2. "Office of the Vice Chancellor". vc.futa.edu.ng. Retrieved 2021-01-15.
  3. 3.0 3.1 "The Vice-Chancellor – MCIU". www.mciu.edu.ng. Archived from the original on 2018-04-13.
  4. "The Vice-Chancellor – MCIU" (in Turanci). 28 May 2018. Archived from the original on 2019-04-17. Retrieved 2019-04-17.
  5. "DID YOU KNOW? Joseph Fuwape, wife are VCs of separate varsities". TheCable Lifestyle (in Turanci). 2022-05-16. Retrieved 2023-06-24.
  6. Women in Physics in Nigeria and Other sub-Saharan African Countries: Progress and Challenges https://absuploads.aps.org/presentation.cfm?pid=14321
  7. Women in Physics in Nigeria and Other sub-Saharan African Countries: Progress and Challenges https://absuploads.aps.org/presentation.cfm?pid=14321
  8. "APS Meeting Presentation". absuploads.aps.org. Retrieved 2020-07-01.
  9. Ogunjo, S. T.; Dada, J. B.; Fuwape, I. A. (2020). "Spatio-Temporal Variation of Nonlinearity in Tropospheric Zenith Wet Delay over West Africa". Telecommunications and Radio Engineering (in Turanci). 79 (11): 1009–1016. doi:10.1615/TelecomRadEng.v79.i11.100. ISSN 0040-2508. S2CID 226617170.
  10. "Robert e. Marshak Lectureship".
  11. "FUTA's Fuwape wins AU scientific award". PM News. 3 March 2021. Retrieved 8 March 2023.
  12. "Fellows nominated in 2022". APS Fellows archive. American Physical Society. Retrieved 2022-10-19.
  13. "FUTA Governing Council Appoints Fuwape as New Vice Chancellor". Allschool (in Turanci). 2017-05-23. Retrieved 2021-01-14.