Harris Eghagha
Birgediya Janar Harris Otadafevwerha Deodemise Eghagha (An haife shi a ranar 8 ga Maris, 1934). An nada shi gwamnan soja a jihar Ogun, Najeriya daga watan Yuli a shekarar 1978 zuwa watan Oktoban 1979 a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo, inda ya mika mulki ga zababben gwamna Olabisi Onabanjo a farkon watan Oktoba. Jamhuriyar Najeriya ta Biyu.[1]
Harris Eghagha | |||
---|---|---|---|
ga Yuli, 1978 - Oktoba 1979 ← Saidu Ayodele Balogun - Olabisi Onabanjo → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Okpe, 8 ga Maris, 1934 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Urhobo (en) | ||
Mutuwa | 19 ga Maris, 2009 | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da hafsa | ||
Digiri | Janar |
Haihuwa
gyara sasheAn haifi Eghagha a ranar 8 ga Maris, 1934 a Mereje, karamar hukumar Okpe, Urhoboland, jihar Delta .
Eghagha ya taka rawa kadan a juyin mulkin watan Janairun 1966 wanda aka hambarar da jamhuriya ta farko a Najeriya kuma ya Haifar da mulkin soja na Manjo-Janar Johnson Aguiyi-Ironsi [2] a matsayin Lieutenant na biyu mai kula da shinkan gen hanya a Kaduna.
Gwamana Jihar Ogun
gyara sasheAn nada shi gwamnan soja a jihar Ogun, Najeriya a Ranar Yuli, 1978 zuwa Oktoban 1979. Yasamu Nasarorin da ya samu a lokacin dayake gwamnan jihar Ogunsun hada da gina rukunin majalisa da hanyoyin sadarwa a Abeokuta, babban birnin jihar. Ya gina tare da kaddamar da Otal din Jihar Ogun, Abeokuta, ya kafa masana’antu a fadin jihar sannan ya kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ogun (yanzu Moshood Abiola Polytechnic ) a Abeokuta. Ya kuma rike mukaddashin Gwamnan Jahohin Sokoto da Kwara, kuma ya kasance Babban Kwamishinan Najeriya a Ghana.
Mutuwa
gyara sasheBirgediya Janar Har[3]ris Eghagha ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas a ranar 19 ga Maris, 2009 yana da shekaru 75.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://military-history.fandom.com/wiki/Harris_Eghagha
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-06-15. Retrieved 2022-06-15.
- ↑ https://archive.ogunstate.gov.ng/public/ogun-state/governors/harris-eghagha[permanent dead link]