Hamza Abu Faris ,(Larabci: حمزة أبوفارس‎), malami ne kuma ɗan siyasa ɗan ƙasar Libya 'wanda aka haife shi a Msallata a ranar 13 ga watan Janairu ,1946.[1] Abdurrahim El-Keib ,ne aka naɗa shi Awqaf & Islamic Affairs ,Minister a ranar 22 ga watan Nuwamba 2011.[2]

Hamza Abu Faris
Rayuwa
Haihuwa Msallata, 13 ga Janairu, 1946 (78 shekaru)
ƙasa Libya
Karatu
Makaranta University of Libya (en) Fassara
Ez-Zitouna University (en) Fassara
Jami'ar Tripoli
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Employers Jami'ar Benghazi
Imani
Jam'iyar siyasa no value


An baiwa Hamza Abu Faris takardar shedar koyarwa a harshen Larabci da koyar da addini daga birnin Tripoli a shekarar 1967. A cikin shekarar 1971 ya sami takardar shaidar sakandare a Sashen Adabi sannan ya ci gaba da karatu a Kwalejin Malamai da Ilimi mai zurfi a Tripoli.[3]


Abu Faris ya samu digirinsa na farko a fannin Harshen Faransanci da adabi bayan ya yi karatu a Sashen Harsuna.

Ya yi karatun digirinsa na biyu a jami'ar Al Fateh a fannin ilimin addinin musulunci ƙarƙashin kulawar Dr. Abd'al-Salaam Abu Naji a shekarar 1984.

A shekara ta 2000 Hamza Abu Faris ya sami digirin digirgir (Ph.D) a fannin Kimiyyar Musulunci, tare da ba da fifiko a fannin Fiqhu (Comparative Fiqh) daga Jami'ar Zaytuna da ke Tunisiya; Kundin karatunsa na digirin digirgir yana da taken "Alkali Abdul Wahab al-Baghdadi da tsarinsa na tafsirin sakon manzon Allah."[4]

Horon Addini

gyara sashe

Dangantakar Hamza Abu Faris da ilimin Shari’a (ilimi da horar da hadisai na shari’a) ta fara ne, a hannun Shaikh wani kauye; ya kammala haddar Alkur'ani a shekarar 1982.

Musamman:

  • Fikihun Malikiyya daga shahararrun ayyukan (al Malik).
  • Tauhid (ka'idar kadaita Allah)
  • Ilimin Hadisi (hadisai dangane da rayuwar Annabi Muhammad)
  • Tafsirin Alqur'ani
  • Muwatta (nassi na asali a mazhabar Malikiyya na fikihu)
  • tafsirinsa al-Zurqani
  • Sahihul Bukhari (Hadisin Hadisai)
  • Sahih Muslim (Tarin Hadithin Canonical)

Kwarewa ta musamman a fagen gado da ilimin fikihu.

Aikin koyarwa

gyara sashe

Hamza Abu Faris ya koyar a matakin sakandire na shekaru da dama kafin ya koyar a tsangayar shari'a a jami'ar Benghazi daga baya kuma ya karantar a bangaren shari'a na jami'ar Nasser ta Tarhuna. Daga baya an naɗa Abu Faris a bangaren shari'a a jami'ar Al Fateh dake birnin Tripoli.

Sauran Ayyuka

gyara sashe

Ya yi aiki a matsayin mai bincike na Majalisar Fiqhu na Kungiyar Ƙasashen Musulmi a Makka da Majalisar Fatawa da Bincike ta Turai.

Ya halarci wani shirin talabijin mai suna Musulunci da salon rayuwa a gidan talabijin na Libya, wanda ake watsa shi kai tsaye a ranakun Juma'a da Asabar.

Manazarta

gyara sashe
  1. Abu Faris, Hamza. "Hamza Abu Faris' Official CV". Archived from the original on 26 April 2012. Retrieved 12 December 2011.
  2. "Libya's NTC unveils new government line-up". Reuters. 22 November 2011. Retrieved 23 November 2011.
  3. "Libya's NTC unveils new government line-up". Reuters. 22 November 2011. Retrieved 23 November 2011.
  4. Abu Faris, Hamza. "Hamza Abu Faris' Official CV". Archived from the original on 26 April 2012. Retrieved 12 December 2011.