Halima Abubakar
Halima Abubakar (an haife ta 12 ga watan Yuni, shekara ta alif 1985)[1] ’yar fim ce ta Nijeriya.[2][3] A shekarar 2011, ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar fim ta Afro Hollywood.[4][5]
Halima Abubakar | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Halima Abubakar |
Haihuwa | Kano, 12 ga Yuni, 1985 (39 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Ebira |
Harshen uwa | Yaren Ebira |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Bayero |
Matakin karatu | Digiri |
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo |
Imani | |
Addini | Musulunci |
IMDb | nm2306517 |
Rayuwar mutum
gyara sasheHalima haifaffiyar garin kano ne amma asalinta daga Kogi.[6] Ta halarci makarantar firamare ta Ideal dake Kano[7] sannan ta karanci ilimin zamantakewar dan Adam a Jami'ar Bayero, Kano. A watan Oktoba, na shekarar 2018, Halima ta bayyana cewa har yanzu ita budurwa ce.[8]
A watan Afrilu, na shekarar 2020, ta sanar da haihuwar danta a shafin ta na Instagram.
Ayyuka
gyara sasheTa fara wasan kwaikwayo ne a shekarar 2001 lokacin da ta taka karama a fim din Rejection. Matsayinta na farko shine jagora a Gangster Paradise. Har ila yau, ita ce Shugabar Kamfanin Nishaɗi ta Modehouse, alamar kiɗa da kamfanin sarrafa nishaɗi.[9]
Fina-finai
gyara sashe- Slip of Fate
- Tears of a Child
- Secret Shadows
- Gangster Paradise
- Area Mama
- Men in Love (film)
- Love Castle
Manazarta
gyara sashe- ↑ In Pictures: Halima Abubakar Birthday Shoot". jaguda.com. 13 June, 2014. Retrieved 14 November, 2021.
- ↑ "I can embarrass you if you get randy with me – Halima Abubakar". vanguardngr.com. 26 April, 2014. Retrieved 7 October 2014. Check date values in:
|date=
(help) - ↑ "Halima Abubakar explodes: Why I fought Tonto Dikeh". modernghana.com. Retrieved 7 October, 2014. Check date values in:
|accessdate=
(help) - ↑ "2face Idibia and Annie Maculay Lighten Up Halima Abubakar Birthday". gistmania.com. 17 June, 2012. Retrieved 7 October 2014. Check date values in:
|date=
(help) - ↑ "Actress Halima Abubakar's cancer support strategy … good or bad?". vanguardngr.com. 23 November, 2012. Retrieved 7 October, 2014. Check date values in:
|accessdate=
and|date=
(help) - ↑ Day I Cried Over My Boyfriend –Actress Halima Abubakar". Daily Sun Newspaper. primenewsnigeria.com. Archived from the original on 12 October, 2014. Retrieved 7 October, 2014.
- ↑ My first…Halima Abubakar". The Punch. Archived from the original on 12 October, 2014. Retrieved 7 October, 2014.
- ↑ http://www.vanguardngr.com/2018/10/i-cant-wait-to-experience-sex-halima-abubakar/
- ↑ Halima Abubakar turns music-entrepreneur". punchng.com. Archived from the original on 12 October 2014. Retrieved 7 October 2014.
Hanyoyin haɗin waje
gyara sashe- Halima Abubakar on IMDb