Teku wani ginshikin bigire ne wanda Allahu (SWT) ya gina, sashi ne wanda ya kunshi duniyar ruwa da yake gudana a doron kasa. Teku ne ma'ajiyar duk wani ruwa da yake gangarowa ta ko wanne bangare a fadin duniya.

Wikidata.svgTeku
Paracas National Reserve, Ica, Peru-3April2011.jpg
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na water area (en) Fassara
Tributary (en) Fassara main stream (en) Fassara da distributary (en) Fassara
Nada jerin list of seas (en) Fassara
Hoto mai motsi wanda yake nuna manyan tekunan duniya biyar dake akwai
wani Teku a ƙasar New Zealand
teku

Ko da yake teku ta rabu gida-gida wato kananan teku zuwa kuma manya kamar irin su tekun atlantika wato Atlantic ocean da kuma tekun maliya wato Red sea kasan cewar teku nan ne matattarar duk wani ruwa, ta kunshi manya-manyan halittun ruwa kama tun daga kifi zuwa wasu halittu na da ban wadanda bamu san su ba. Bayan haka dandanon ruwan teku ya kasan ce mai gishiri-gishiri ne ba kamar yadda ruwan rijiya yake ba.

Masana ilimin kimiyya sun tabbatar da cewa inda ruwa ya mamaye ya fi India kasa ta mamaye. A bisa kididdiga inda ruwa ya mamaye ya kai kashi saba'in da biyar cikin dari (75%), amma inda kasa ta mamaye kwata-kwata kashi ashirin da biyar ne cikin dari (25%).

Amfanin TekuGyara

 
Ana amfani da teku don tafiye-tafiye
 
Tafiye tafiye cikin teku

Teku ya kasance babban kundi inda dan adam ke amfani dashi a rayuwarsa, ana amfani da teku domin tafiye-tafiye a cikin jiragen ruwa daga kasa zuwa kasa ko daga wata nahiya zuwa wata nahiyar.

Sannan kuma akwai hallitun ruwa da ake samu daban-daban kamar su kifi, dorinar ruwa, da dai sauransu, haka zalika man fetur shima duk daga teku ake samo shi da kuma irinsu gwala gwalai da dai abubuwa masu dimbin amfani ga Yan-adam

ManazartaGyara

Wannan Muƙalar guntu ne: yana buƙatar a inganta shi, kuna iya gyara shi.