Doris Uzoka-Anite
Doris Nkiruka Uzoka-Anite (an haifeta ranar 16 ga watan Oktoba, 1981) yar siyasar Najeriya ce, likita kuma kwararra kan harkokin kuɗi, wacce ta taɓa riƙe muƙamin ministar Ma'aikatar Masana'antu, Kasuwanci da Saka hannun jari na Najeriya tun 2023.[1]
Doris Uzoka-Anite | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Imo, 16 Oktoba 1973 (51 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar jahar Benin |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa, Ma'aikacin banki da likita |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Doris Nkiruka Uzoka a ranar 16 ga Oktoba 1981 a Orsu-Obodo, Oru Clan, Oguta, Jihar Imo, Najeriya. Ta yi karatunta a fannin likitanci a Jami'ar Benin kuma ta zama ƙwararriyar likita a shekara ta 1999.[1] Daga baya, ta sami takardar shedar Chartered Financial Analyst (CFA).
Sana'a
gyara sasheUzoka-Anite ta fara aikinta na banki a sashin bankin Zenith Bank Corporate Social Responsibility (CSR) sannan ta jagoranci sashen horar da ma'aikata da horarwa. A cikin 2011, ta canza zuwa (Treasury) kuma daga baya aka naɗa ta ma'ajin bankin a shekarar 2017.[1] A watan Maris 2021, Gwamna Hope Uzodinma ya naɗa ta kwamishiniyar kuɗi kuma ko’odinetan tattalin arziki ta jihar Imo.[2][3]
A ranar 27 ga Yuli, 2023, ta kasance ɗaya daga cikin su 28 na farko da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aika wa majalisar dattawa domin tantancewa.[4]
A ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, 2023, Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da ita a matsayin ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari na Tarayyar Najeriya.[5][6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 Ekugo, Ngozi (27 July 2023). "Meet Dr. Doris Anite, a medical doctor turned banker, now a ministerial nominee". www.nairametrics.com.
- ↑ Alozie, Chinonso (March 11, 2020). "Imo commissioners' list out". www.vanguardngr.com.
- ↑ Princely, Onyenwe (24 March 2021). "Meet Imo Commissioner for Finance, Dr.(Mrs). Doris Nkiruka Uzoka Anite (Photos)". www.9newsng.com.
- ↑ Bada, Yusuf (27 July 2023). "Ministerial List: Full List of 28 Nominees President Tinubu Sends to Senate". www.legit.ng.
- ↑ "Doris, Wike, Umahi, Bosun and Pate makes list of super Ministers to watch out for". www.guardian.ng. 20 August 2023. Archived from the original on 21 September 2023. Retrieved 20 November 2023.
- ↑ "We are ready to open Nigeria for more business investments – Uzoka-Anite". www.vanguardngr.com. Retrieved 21 August 2023.