Bala Mohammed

Ɗan siyasar Najeriya

Bala Mohammed (Inkiya Kauran Bauchi) An haife shi ne a farkon Watan Oktoban shekarar ta alif dari tara da hamsin da takwas, 1958)[1] Miladiyya.(A.c) Bala Mohammed yayi karatu ne a gida har ya samu Digiri a harshen Turanci a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1982, Bala Mohammed ya soma aiki ne a matsayin mai kawowa gidan jaridar nan ta The Democrat rahoto a shekarar 1983 Bio[permanent dead link] bayan ya kammala karatu. Daga nan kuma Mohammed ya koma aikin gwamnati har zuwa shekarar 2000, Bala Mohammed yayi aiki a ma’aikatu daban-daban wanda su ka haɗa da Ma’aikatar ma’adanai da ta harkokin cikin gida, da Ma’aikatar harkokin jirgin sama. A ƙarshe dai yayi ritaya a matsayin Darekta a Nigerian Meteorological Agency. Bala Mohammed ya shiga siyasa ne bayan yayi ritaya inda yayi takara, ya kuma ci kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a shekarar 2007. Sanatan na ANPP ya samu matsala da tsohon Mai gidan sa watau Gwamna Isa Yuguda wanda ya koma PDP a mulkin Yar'adua. Labarai LABARAI Takaitaccen tarihin Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi mai jiran-gado Talata, Maris 26, 2019 at 7:04 Safiya by Muhammad Malumfashi A jiya ne hukumar zaɓe na INEC ta sanar da cewa Sanata Bala Mohammed ne ya lashe zaɓen gwamna da aka yi a jihar Bauchi inda ya doke gwamna mai-ci. Mun kawo kaɗan daga tarihin Kauran Bauchi News.

Bala Mohammed
Gwamnan Jihar Bauchi

29 Mayu 2019 -
Mohammed Abdullahi Abubakar
ma'aikatar Babban birnin tarayya

11 ga Yuli, 2011 - 29 Mayu 2015 - Mohammed Musa Bello
District: Bauchi South
ma'aikatar Babban birnin tarayya

8 ga Afirilu, 2010 - 11 ga Yuli, 2011
Adamu Aliero
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

8 ga Afirilu, 2007 - 8 ga Afirilu, 2010
Rayuwa
Cikakken suna Bala Mohammed
Haihuwa Alkaleri, 5 Oktoba 1958 (66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
  1. Haihuwa da karatu An haifi Bala Abdulkadir Mohammed ne a farkon Watan Oktoban 1958, kenan yana da shekaru 60 yanzu a Duniya. Bala Mohammed yayi karatu ne a gida har ya samu Digiri a harshen Turanci a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1982.
  2. Aikace-aikace Sanata Bala Mohammed ya soma aiki ne a matsayin mai kawowa gidan jaridar nan ta The Democrat rahoto a 1983 bayan ya kammala karatu. Daga nan kuma Mohammed ya koma aikin gwamnati har zuwa shekarar 2000.
  3. Aikin Gwamnati Bala Mohammed yayi aiki a ma’aikatu daban-daban wanda su ka haɗa da Ma’aikatar ma’adanai da ta harkokin cikin gida, da Ma’aikatar harkokin jirgin sama. A ƙarshe dai yayi ritaya a matsayin Darekta a (Nigerian Meteorological Agency). Sabon gwamnan ya kuma yi aiki a hukumar da ke kula da jirgin kasa a Najeriya watau (Nigerian Railway Corporation) daga shekara ta 2005 har 2007. Kafin nan kuma yayi aiki da Isa Yuguda a matsayin mai ba sa shawara daga 2000 zuwa 2005.
  4. Siyasar Bala Mohammed ya shiga siyasa ne bayan yayi ritaya inda yayi takara, ya kuma ci kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a 2007. Sanatan na ANPP ya samu matsala da tsohon Mai gidan sa watau Gwamna Isa Yuguda wanda ya koma PDP a mulkin 'Yaradua. A shekarar 2010 ne shugaban kasa na rikon kwarya watau Goodluck Jonathan ya nada Bala Mohammed a matsayin Ministan babban birnin tarayya Abuja har zuwa 2015. Sanatan yana cikin waɗanda suka fara cewa a naɗa Jonathan kan mulki a wancan lokaci. A zaɓen 2019 ne Bala Mohammed ya doke gwamna Mohammed Abubakar, na jam’iyyar APC inda ya samu kuri’u 515,113. APC ta samu kuri’a 500,625 ne a zaɓen inji hukumar INEC mai zaman kan-ta.

Nijeriya .[2][3][4][5][6][7]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.bing.com/ck/a?!&&p=51a91d0d264d5da3JmltdHM9MTcxOTEwMDgwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTI4Mw&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Bala+Mohammed+biography&u=a1aHR0cHM6Ly93d3cuYmF1Y2hpc3RhdGUuZ292Lm5nL2dvdmVybm9ycy1wcm9maWxlLw&ntb=1
  2. "Wane ne Bala Muhammad Kauran Bauchi?". BBC Hausa.Com. 24 January 2020. Retrieved 20 November 2021.
  3. Ali, Rechard (29 April 2010). "Denudation: Remembering Dr Bala Mohammed". pambazuka.org. Retrieved 30 November 2021.
  4. "Kaura Economic Empowerment Programme Keep In Bogoro and Tafawa balewa L.G.A". Naijabasic.ng. 15 January 2022. Archived from the original on 8 February 2023. Retrieved 20 April 2022.
  5. "Gov. Bala Mohammed has Constructed 2,500 housing units to reduce housing deficit in Bauchi State". Naijabasic.ng. 17 January 2022. Archived from the original on 8 February 2023. Retrieved 20 April 2022. Cite has empty unknown parameter: |6= (help)
  6. "Governor Bala Mohammed constructed over 500 classrooms in Bauchi State to enhance education". Naijabasic.ng. 31 January 2022. Archived from the original on 1 October 2022. Retrieved 20 April 2022.
  7. Labaranyau.com (2022-04-27). "Duk Yen Takarar Shugabancin Nijeriya Bawanda Yakai Bala Muhammad – Kungiyar Niger Delta". Bala MD. line feed character in |title= at position 28 (help)