Anthony Anenih
Anthony Akhakon "Tony" Anenih (4 Agusta 1933 - 28 Oktoba 2018) ɗan siyasan Najeriya ne wanda aka naɗa Ministan Ayyuka da Gidaje a shekara ta 1999.[1]
Anthony Anenih | |||
---|---|---|---|
1999 - 2003 - Adeseye Ogunlewe → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 4 ga Augusta, 1933 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | 28 Oktoba 2018 | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Anenih a Uzenema-Arue a garin Uromi, A shekarar 1933 ya shiga aikin ƴan sandan Najeriya a birnin Benin. Yana aiki a gida, ya sami shaidar kammala karatun sakandare. Ya halarci kwalejin ƴan sanda a Ikeja, kuma an zaɓe shi don ƙarin horo a Kwalejin 'yan sanda na Bramshill, Basingstoke, Ingila a 1966 da Makarantar 'Yan sanda ta Duniya, Washington DC a 1970.[2] Ya yi aiki a matsayin ɗan sanda mai bin doka da oda ga Gwamna Janar na farko a Najeriya, Dr. Nnamdi Azikiwe. Ya yi aiki a matsayin malami a kwalejojin ƴan sanda daban-daban, sannan a shekarar 1975 aka tura shi Kwalejin Gudanarwa (ASCON), Legas. Ya yi ritaya daga aikin ƴan sanda a matsayin kwamishinan ƴan sanda.[3]
Farkon siyasa
gyara sasheAnenih ya kasance shugaban jam'iyyar NPN na jihar tsakanin 1981 zuwa 1983, inda ya taimaka wa Dr. Samuel Ogbemudia ya zama gwamnan farar hula na jihar Bendel. Duk da haka, an kwace kujerar gwamna a lokacin da sojoji suka karbe watan Disamba shekara ta 1983. Ya kasance shugaban jam’iyyar Social Democratic Party na ƙasa daga 1992 zuwa 1993, lokacin da ya taimaka wajen zaɓen Cif MKO Abiola a matsayin shugaban ƙasa. Ya kasance memba na taron tsarin mulki a 1994.[3]
Anenih ya kasance mamba a jam'iyyar Peoples Democratic Movement (PDM), United Nigeria Congress Party (UNCP) da kuma People's Democratic Party (PDP). Anenih an ce shi ne ya kitsa sanarwar Shugaba Obasanjo a ranar 26 ga Afrilu, 2002 a babban taron kasa da kasa Abuja.[4] Ya kasance mataimakin kodinetan ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Olusegun Obasanjo na ƙasa a zabukan shekarun; 1999 da 2003.[3]
Ministan Ayyuka da Gidaje
gyara sasheAn naɗa Cif Anenih Ministan Ayyuka da Gidaje a shekarar 1999. Daga nan ya zama shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP.[3]
Rigingimu
gyara sasheA watan Oktoban 2009, kwamitin majalisar dattijai ya fitar da rahoto kan binciken da suka yi na amfani da sama da Naira biliyan 300 a harkar sufuri a lokacin gwamnatin Obasanjo. Kwamitin ya ba da shawarar gurfanar da tsoffin Ministoci goma sha uku da suka haɗa da Anenih, inda ya ce ya bayar da kwangiloli ba tare da tanadin kasafin kuɗi ba.[5] A cikin watan Nuwamba 2009, Majalisar Dattijai ta ki amincewa da rahoton ba tare da bata lokaci ba.[6]
A watan Oktoban shekarar 2009, babban bankin Najeriya ya fitar da jerin sunayen abokan hulda da ke da manyan basussuka ga wasu bankuna biyar da aka tantance kwanan nan. Ta ruwaito cewa, ta hanyar Mettle Energy and Gas Limited, Cif Tony Anenih da Osahon Asemota sun ci bashin Naira miliyan 2,065.[7] Anenih ya ce babu ruwansa da kamfanin Mettle Energy and Gas Limited, kuma ya ce ya rubutawa shugabar hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Farida Waziri, inda ya buƙaci hukumar ta binciki lamarin.[8]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheYa auri Josephine Anenih, lauya, wacce ita ce shugabar ƙungiyar lauyoyin mata daga 1994 zuwa 2000. An naɗa ta a matsayin ministar harkokin mata a ranar 6 ga Afrilun 2010, lokacin da muƙaddashin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana sabuwar majalisarsa.[9]
Mutuwa
gyara sasheAnenih ya mutu ranar 28 ga watan Oktoban 2018, kuma an binne shi a mahaifarsa da ke Uromi, inda aka binne shi ya samu halartar manyan mutane a ƙasar. Har zuwa rasuwarsa, shi ne Iyasele na Esan Land.[10]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Bello, Elijah (2018-11-04). "From policeman to political juggernaut: The story of Anthony Anenih". Businessday NG (in Turanci). Retrieved 2023-01-29.
- ↑ "OBITUARY: Tony Anenih: Nigeria's 'Mr Fix It'" (in Turanci). 2018-10-29. Retrieved 2022-03-17.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 Tony Ikpasaja (4 August 2009). "Anenih: Driving Nigeria From Uromi". Leadership Nigeria. Archived from the original on 13 July 2011. Retrieved 2009-11-27.
- ↑ Seyi Oduyela. "Alhaji Abubakar Atiku: The Face Of An Opportunist". Dawodu. Archived from the original on 2 January 2010. Retrieved 2009-11-27.
- ↑ "N300 Billion Transportation Contracts - Senate Report Indicts Anenih, Okonjo-Iweala, Ciroma". Vanguard. 12 October 2009. Archived from the original on 15 October 2009. Retrieved 2009-11-27.
- ↑ Emmanuel Aziken (5 November 2009). "Senate suspends N300bn contract report". Vanguard. Retrieved 2009-11-27.
- ↑ ISAAC ANUMIHE; OMODELE ADIGUN; MADUKA NWEKE; KELECHI MGBOJI; TITUS NWOKOJI; LOUIS IBA (16 October 2009). "CBN releases fresh debtors' list, includes Marwa, Pat Utomi, Tony Anenih, Fasawe". OnlineNigeria. Archived from the original on 25 February 2012. Retrieved 2009-11-27.
- ↑ Yusuf Alli (2009-10-16). "Anger, shock over list of troubled banks' debtors". The Nation. Archived from the original on 26 July 2011. Retrieved 2009-11-27.
- ↑ "Ministers - the Profiles". ThisDay. 7 April 2010. Archived from the original on 11 April 2010. Retrieved 2010-04-14.
- ↑ "Dogara mourns Tony Anenih". Archived from the original on 24 January 2019. Retrieved 24 January 2019.