Moshood Abiola

Ɗan kasuwa,ɗan siyasan, mawallafi (1937-1998)

Moshood Kashimawo Olawale Abiola, Babban Kwamandan Askarawan Tarayya (GCFR) (Ya rayu daga ranar 24 ga watan Agusta, a shekara ta 1937 zuwa ranar 7 ga watan shekara ta 1998) Dan Nijeriya ne, Bayarabe Dan kasuwa, mawallafi, dan siyasa, kuma mai juya al'amurran Yoruban Egba, shi ne Aare Ona Kankafo na kasar Yarbawa.[1] MKO Abiola ya nemi shugabancin Nijeriya a zaben shugabancin Najeria na shekara ta 1993, wanda sakamakon zaben shugaban kasa na waccan lokaci na soji Ibrahim Babangida ya ki yarda da shi, saboda zargin tabka magudi ta aikata ba dai-dai ba.[2] Sai dai a 6 ga watan Yuni shekarar 2018 shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa Abiola nasarar zabensa kuma ya zama daga cikin shugaban kasar Nijeriya, har ma ya sa ranar "12 ga watan Yuni" ta zamanto ranar dimokradiya a Nijeriya, wadda aka canja daga 29 na watan Mayu.[3][4]

Moshood Abiola
Rayuwa
Haihuwa Abeokuta, 24 ga Augusta, 1937
ƙasa Najeriya
Mutuwa Abuja, 7 ga Yuli, 1998
Yanayin mutuwa kisan kai
Ƴan uwa
Abokiyar zama Remi Abiola
Kudirat Abiola
Yara
Karatu
Makaranta Baptist Boys’ High School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Majalisar Najeriya da Kamaru
kafin zaben 1993 da aka soke

Abiola ya kasance aboki na kud-da-kud ga shugaba Babangida[5] sannan kuma ya taimaka dan ganin Babangida ya zama shugaban kasar Nijeriya. Karbuwar da Abiola ya samu a zaben da aka gudanar a watan "Yuni" a shekara ta 1993 ya zo ne daga ko'ina a cikin yankuna da shiyoyin Nijeriya da addinai.[6] A lokacin rasuwarsa, ya zama wani abun nuni ga dimokradiyar Nijeriya.[7]

Mutum-mutumin Moshood Abiola
Wani kamu da aka masa

Manazarta gyara sashe

  1. Cite news|url=https://www.vanguardngr.com/2017/10/ona-kakanfos-origin-myth-power-prof-banji-akintoye/%7Ctitle=Are Ona Kakanfo's origin, myth and power by Prof. Banji Akintoye - Vanguard News|date=2017-10-22|work=Vanguard News|access-date=2018-08-15|language=en-US
  2. Hamilton, Janice. Nigeria in Pictures, p. 70.
  3. cite news |title=UPDATED: Buhari declares June 12 Democracy Day, honours MKO Abiola with GCFR |url=http://punchng.com/breaking-buhari-declares-june-12-democracy-day-honours-abiola-with-gcfr/ |accessdate=6 June 2018 |work=Punch Newspapers
  4. cite news |title=BREAKING: Buhari declares June 12 Democracy Day to honour Abiola |url=https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/271397-breaking-buhari-declares-june-12-democracy-day-to-honour-abiola.html |accessdate=6 June 2018 |work=Premium Times Nigeria |date=6 June 2018
  5. Rufai, Misbahu. (1990, May 11). A man called MKO. Muslim Journal.
  6. Holman, Michael, and Michela Wrong. "Chief Moshood Abiola Presumed Poll Winner Managed to Straddle the Regional and Religious Split in a Way Few Nigerian Politicians Can Do Today." Financial Times, 8 July 1998, p. 3. Financial Times Historical Archive.
  7. Cite book|url=https://www.worldcat.org/oclc/813166032%7Ctitle=This house has fallen : Nigeria in crisis|last=1957-|first=Maier, Karl,|date=2002|publisher=Westview Press|isbn=9780786730612|location=Boulder, Colo.|oclc=813166032