Aminu Bashir Wali
Aminu Bashir WaliAminu Bashir Wali (Taimako·bayani) (an haife shi ne a ranar 3 ga watan Agustan, shekara ta alif ɗari tara da arba'in da daya 1941A.c) ya taba riķe mukamin ministan harkokin waje na Najeriya daga shekarar 2014 zuwa shekara ta 2015.[1]
Aminu Bashir Wali | |||||
---|---|---|---|---|---|
2014 - 2015 ← Viola Onwuliri - Geoffrey Onyeama →
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | jahar Kano, 3 ga Augusta, 1941 (83 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Hausawa | ||||
Harshen uwa | Hausa | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | University of North London (en) | ||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa |
Tarihin rayuwa
gyara sasheAn haifi Wali a cikin garin Kano a shekara ta 1941. Ilimin nasa ya hada da samun horo a Makarantar Koyon Larabci da ke Kano kuma ya kammala a shekara ta 1967 tare da digiri a kan Gudanar da Harkokin Kasuwanci daga North-Western Polytechnic da ke Landan. [2]
Ayyuka
gyara sasheDaga shekara ta 2004, ya kasance wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya . Sannan ya zama Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Jama'ar Sin wato China.
An nada Wali a matsayin Ministan Harkokin Kasashen Waje a karkashin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan . Tafiye-tafiye zuwa kasashen waje sun hada da guda daya zuwa Turkiyya, bayan gayyatar da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya yi . [3] A watan Oktoban shekara ta 2014, Wali ya karbi Ministocin Harkokin Wajen na Jamus da Faransa, Frank-Walter Steinmeier da Laurent Fabius, don tattaunawa kan sace-sacen Boko Haram da matakan yaki da barkewar cutar Ebola .
'Yan uwan juna
1, Abubakar Bashir Wali
2, Mahe Bashir Wali
3, Umar Bashir Wali
4, Mustapha Bashir Wali
Duba kuma
gyara sashe- Ministan Harkokin Waje (Najeriya)
Manazarta
gyara sashe- ↑ "The Honourable Minister of Foreign Affairs Mr. Geoffrey Onyeama". Ministry of Foreign Affairs of Nigeria. Archived from the original on 2016-08-12. Retrieved 10 February 2016.
- ↑ Biographical Notes, UNVienna, Retrieved 10 February 2016
- ↑ No: 6, 07 January 2015, Press Release Regarding the Visit of H.E. Aminu Bashir Wali, Minister of Foreign Affairs of the Federal Republic of Nigeria Archived 2016-02-16 at the Wayback Machine, Retrieved 10 February 2016