Geoffrey Onyeama
Geoffrey Jideofor Kwusike Onyeama (An haife shi ne a 2 ga watan Fabrairun shekarar ta 1956) ya kasance shi ne Ministan Harkokin Wajen Najeriya. Onyeama an nada shi Ministan Harkokin Wajen Najeriya ne a watan Nuwamba na shekarar ta 2015, Akarka shin Shugaba Muhammadu Buhari . [1]
Geoffrey Onyeama | |||||
---|---|---|---|---|---|
21 ga Augusta, 2019 - 2023
11 Nuwamba, 2015 - 21 ga Augusta, 2019 ← Olugbenga Ashiru | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | jahar Enugu, 2 ga Faburairu, 1956 (68 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƴan uwa | |||||
Mahaifi | Charles Onyeama | ||||
Ahali | Dillibe Onyeama (en) | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
London School of Economics and Political Science (en) Columbia University (en) St John's College (en) | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheOnyeama ya kasan ce ya fito daga dangin masanin shari'ar Najeriya Charles Onyeama.[2] Yayi digirinsa na farko, ya kuma Rike (BA) a Kimiyyar Siyasa daga Jami'ar Columbia, New York a shekarar ta 1977, ya kuma gama digirinsa na farko a bangaran Arts (BA), ya karanci Lauya a Kwalejin St John's College, Cambridge A shekara ta 1980. Yana da Digiri na biyu (LL. M) daga Makarantar Tattalin Arziki da Kimiyyar Siyasa ta London a shekarar ta 1982 , da kuma zama kwararre a bangaren Arts (MA) , da Shari'a daga St John's College, Cambridge a shekara ta 1984.[3] Onyeama an shigar da shi a matsayin Lauya na Kotun Koli ta Nijeriya a cikin shekarar ta1983 kuma an kira shi zuwa ga Ingilishi Bar na Grey's a shekarar ta 1981.[4]
Ayyuka
gyara sasheOnyeama ya fara aikin sa ne a matsayin Jami'in Bincike a Hukumar sake fasalin Dokokin Najeriya a Legas daga shekarar ta 1983 zuwa shekarar ta 1984. Sannan ya yi aiki a matsayin lauya tare da .Mogboh and Associate a Enugu, Nijeriya daga shekara ta 1984 zuwa ta 1985, A shekarar ta 1985, ya shiga Kungiyar World Intellectual Property Organization wato (WIPO) a matsayin Mataimakin Jami'in Shirye-shiryen ci gaban hadin gwiwa da alakar waje, Ofishin Afirka da Yammacin Asiya. Ya sami matsayi a WIPO ya zama Mataimakin Darakta Janar na sashen bunkasa a shekarar ta 2009. A watan Nuwamba na shekarar ta 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi Ministan Harkokin Wajen Najeriya.[5]
Rayuwar mutum
gyara sasheOnyeama ya yi aure; kuma yana da yara uku. da Matarsa ta yanzu ita ce Sulola; wanda Onyeama ke da yara biyu. da ita, Onyeama ya auri ɗiyar Christian Onoh : Nuzo Onoh kuma suna da ɗa na farko da matar. Onyeama mai suna Candice Onyeama; mai rubutun allo da shirya fim.[6][7][8]
A ranar 19 ga watan Yulin na shekara ta 2020, Onyeama ya shiga keɓewar likita bayan ya sanar da cewa ya samu tabbataccin COVID-19.[9] A ƙarshen watan Agusta na shekara ta 2020, Onyeama ya warke daga cutar COVID-19 na coronavirus; kuma ya koma aikinsa na jagoranci a matsayin HMFA: Mai girma Ministan Harkokin Waje a Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya.[10][11][12]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ Ekott, Ini. "UPDATED: Buhari assigns Ministers; Fashola heads Power and Works, Amaechi gets Transportation". Premium Times. Retrieved 30 January 2016.
- ↑ "Geoffrey Onyeama: 7 Things You Should Know About Nigeria's Foreign Affairs Minister". Nigerian Monitor. Retrieved 30 January 2016.
- ↑ "CURRICULUM VITAE OF MR. GEOFFREY ONYEAMA" (PDF). Global Intellectual Property Center. Retrieved 30 January 2016.
- ↑ "CURRICULUM VITAE OF MR. GEOFFREY ONYEAMA" (PDF). Global Intellectual Property Center. Retrieved 30 January 2016.
- ↑ "The Honourable Minister of Foreign Affairs Mr. Geoffrey Onyeama". Ministry of Foreign Affairs of Nigeria. Archived from the original on 12 August 2016. Retrieved 30 January 2016.
- ↑ "Meet Geoffrey Onyeama and his Beautiful Wife Sulola". Nigeria Opera News. Archived from the original on 25 October 2021. Retrieved 20 September 2020.
- ↑ "Norwich Film Festival: Born Again Directed by Candice Onyeama". Norwach Film Festival: United Kingdom. Retrieved 20 September 2020.
- ↑ "Question and Answer With Candice Onyeama Director Screening Short Fiction Born Again". Barnes Film Festival: United Kingdom. Retrieved 20 September 2020.[permanent dead link]
- ↑ "Nigerian Foreign Minister Onyeama tests positive for coronavirus". July 19, 2020. Archived from the original on July 19, 2020. Retrieved November 24, 2020 – via af.reuters.com.
- ↑ "Foreign Minister Geoffrey Onyeama Recovers from Covid-19". The Guardian Nigeria. Archived from the original on 29 September 2020. Retrieved 20 September 2020.
- ↑ "Foreign Minister Onyeama Recovers from COVID-19". Channels Television Nigeria. Retrieved 20 September 2020.
- ↑ "Foreign Minister Geoffrey Onyeama Recovers from COVID-19". Vanguard Nigeria News. Retrieved 20 September 2020.