Ali Reza Tavassoli
Ali Reza Tavassoli | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1962 |
ƙasa | Afghanistan |
Mutuwa | Golan Highest/ Qunitera (en) , 28 ga Faburairu, 2015 |
Sana'a | |
Sana'a | soja |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Ali Reza Tavassoli ( Persian </link> ; 1962 - 28 ga Fabrairu 2015) ɗan ngwagwarmayar ne na kasar Afganistan na Brigade Fatemiyoun . Dan kabilar Hazara, an haife shi ne a kasar Afganistan sannan ya koma Iran inda ya yi karatu a jami'ar Al-Mustafa International University . Ayyukansa na farko a matsayinsa na mayaka shi ne lokacin yakin Iran da Iraki, lokacin da shi da sauran musulmi 'yan Shi'a da dama na Afganistan suka shiga cikin dakarun sa kai masu goyon bayan Iran don yakar Iraki . Bayan juyin juya halin Larabawa a shekara ta 2011, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun nada Tavassoli don jagorantar mayakan Shi'a na Afghanistan a yakin basasar Syria . Shekaru hudu bayan haka, yayin da suke yaki tare da IRGC, Hizbullah, da gwamnatin Siriya a hare-haren Kudancin Siriya, Jabhat al-Nusra ya kashe shi . [1]
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Tavassoli a shekara ta 1962 a Afghanistan . [2] Daga bisani ya koma kasar Iran inda ya zauna a birnin Mashad ya yi karatu a birnin Qum inda daga karshe ya kammala jami'ar Al-Mustafa International University . [3]
Sana'a
gyara sasheYa yi aiki a matsayin mayaka na sa kai na Shi'a a bangaren Iran a yakin Iran-Iraki . [4]
A lokacin yakin basasar Siriya Qasem Soleimani wanda tsohon kwamandan dakarun Quds ne na Iran ya nada Tavassoli a matsayin kwamandan mayakan sa kai na Shi'a daga Afghanistan, Iraki, Pakistan, Lebanon, Siriya da Yemen . A shekara ta 2014, ya shirya 'yan sa kai na 'yan Shi'a na Afganistan tare da kafa rundunar Fatemiyoun Brigade don kare wuraren ibadar Shi'a a kasar Siriya, inda aka yi masa lakabi da Larabci Abu Hamed. [1] [3]
Mutuwa
gyara sasheA ranar 28 ga Fabrairun 2015, an kashe Tavassoli a lokacin farmakin kudancin Siriya a lokacin da yake fafatawa da Jabhat al-Nusra a Daraa, kudancin Damascus . [5] [1] An binne shi a birnin Mashad na kasar Iran. [3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 Neriah, Jacques (4 March 2015). "Iran Deploys Afghan Shiite Brigade to Spread Its Control in Southern Syria". Jerusalem Center for Public Affairs. Retrieved 3 April 2016. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "JCPA" defined multiple times with different content - ↑ Zohuri, Vahid (15 March 2015). "Ali Reza Tavassoli, Afghan commander of Fatemiyoun Brigade". Kayhan. Retrieved 3 April 2016.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 Esfandiari, Golnaz (25 April 2015). "Increasing Number Of Afghans, Pakistanis Killed In Syria Buried In Iran". Persian Letters. Retrieved 3 April 2016. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "PersianLe" defined multiple times with different content - ↑ Alfoneh, Ali (3 August 2015). "Shiite Combat Casualties Show the Depth of Iran's Involvement in Syria". Washington Institute for Near East Policy. Retrieved 3 April 2016.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs nameddailystar