Qaseim Suleimani
Qasem Soleimani ( An haife shi a ranar 11 ga watan Mayu a shekara ta 1957 – ya mutu a ranar 3 ga watan Janairu shekara ta 2020), kuma ana ce mai (Qassim Soleimani), ya kasance manjo janaral a kasar Iran a wata gidauniyar kasan mai suna Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) kuma tin daga a shekara ta 1998 har zuwa mutuwan shi ya kasance kwamandan rundunan Quds.
Soleimani ya fara aikin sojane tin a yakin Iran da Iraq a shekara ta 1980, wanda a lokacin yana umartan runduna na 41. An kashe Soleimani ne da wata jirgi mara mahayi, wacce ake sarrafa ta da na'ura, a ranar 3 ga watan Janairu shekarar 2020 a Bagadaza, wanda tsohan shugaban kasan Amurka Donal Trump ya rattaba hannu.
Abokiyar Zama
gyara sasheAbokiyar zaman manjor janar Qasem soleimani sunan ta Zainab Soleimani.
Iyalan Sa
gyara sasheYakasance yanada yara kaman haka, Zainab soleimani, Sohrab Suleimani, Fatemah Suleimani, Muhammad Reza Suleimani, Ahmed Suleimani.