Aisha Dahiru Ahmad

Ƴar Siyasar Najeriya
(an turo daga Aishatu Dahiru Ahmed)

Aishatu Dahiru Ahmed, ( Augusta 1971) wacce aka fi sani da Binani, ‘yar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa. Tsohuwar Sanata ce data wakilci Adamawa ta tsakiya a majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin Tutar jam'iyyar APC mai alamar tsintsiya. Sa'annan tayi takarar gwamna a shekarar 2023 ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC.

Aisha Dahiru Ahmad
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
Aisha Dahiru Ahmad - AMINU IYA ABBAS (en) Fassara
District: Adamawa Central
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: Yola North/Yola South/Girei
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
Rayuwa
Cikakken suna Aishatu Dahiru Ahmed
Haihuwa Jahar Kaduna, 11 ga Augusta, 1971 (53 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Southampton (en) Fassara
Jami'ar Jihar Nasarawa
Harsuna Turanci
Fillanci
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da injiniyan lantarki
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress
Aishatu Binani

Farkon Rayuwa

gyara sashe
An haifi Aisha a ranar 11 ga watan Agusta, shekara ta alif ɗari tara da saba'in da  ɗaya 1971A.c. Ta taba zama ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a matsayin mamba a jam’iyyar People’s Democratic Party tsakanin shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.

Aisha Binani ta yi karatun firamare da sakandare a jihar Kaduna kafin ta wuce Jami’ar Southampton, inda ta samu digiri na uku a fannin Eleteical Engineering.[1]


Binani ta kafa kamfanin Binani Nigeria Limited, ƙungiyar Binani Group of Companies da nufin bunkasa da inganta tattalin arziƙin yankin Arewa maso Gabasa a ƙasar Najeriya.

Ta shiga harkar siyasa ne a shekarar 2011 lokacin da aka zaɓe ta a matsayin ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya Daga jihar, Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Daga baya ta sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ta tsaya takarar Sanata inda ta lashe zaɓen kujerar a matsayin  sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya.
A matsayinta na yar majalisar dattijai, Binani ta yi aiki a matsayin shugabar kwamitin majalisar dattawa kan manufofin ci gaba mai dorewa (SDGs).[2]

Takarar Gwamna

gyara sashe

Sanata Aisha Dahiru Ahmed Binani ta lashe tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Adamawa inda ta doke maza shida da kuma jiga-jigan siyasar Jihar Adamawa.

A zaɓen fidda gwanin dai, Binani ta samu kuri’u 430, wanda ya zama mafi rinjaye a zaɓen, inda ta doke Nuhu Ribadu,[3] tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Action Congress kuma Tsohon shugaban hukumar Yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC na farko, wanda ya samu ƙuri’u 288.
Muhammadu Jibrilla Bindow, gwamna mai barin gado ya zo na uku da ƙuri’u 103, Abdurrazaq Namda ya zo na biyu da ƙuri’u 94 sai Wafari Theman da 39.
Wafarniyi Theman da Umar Mustapha Madawaki ne suka samu matsayi na biyar da shida a zaben fidda gwanin.[4]
A ranar 14 ga Oktoba, 2022, wata babbar kotun tarayya da ke Yola ta soke takarar Binani a matsayin yar  takarar gwamnan Jihar Adamawa ta jam’iyyar APC.[5]

Hukuncin da kotun ta yanke, ta bayyana cewa babu dan takarar jam’iyyar APC a jihar a zaben 2023 amma ta ce masu kara da wadanda ake kara suna da damar daukaka kara kan hukuncin.[6] Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa.

Mista Fintiri ya lashe zaben cike gurbin da kuri'u 9,337.  Ya kayar da babbar abokiyar hamayyar sa, Aisha Dahiru, wanda aka fi sani da Binani, ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ta zo ta biyu a zaben da kuri’u 6,513.[7]

A babban zaben da aka gudanar da kuma zaben da aka sake Fintiri na Jam'iyyar PDP ya samu kuri’u 430,861 yayin da yar takarar APC ta samu kuri’u 398,788.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.shineyoureye.org/person/aishatu-dahiru-binnan
  2. https://hausa.leadership.ng/tikitin-tsayawa-takarar-aisha-binani-ya-karfafa-siyasar-matan-arewa/
  3. https://www.thecable.ng/history-as-aishatu-binani-beats-ribadu-bindow-to-adamawa-apc-guber-ticket/amp/
  4. https://dailytrust.com/seven-things-to-know-about-aisha-binani/
  5. https://www.google.com/amp/s/www.bbc.com/hausa/articles/cndrdjgegj8o.amp
  6. https://www.bbc.com/pidgin/articles/czq3dg723ewo
  7. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/594019-updated-inec-declares-pdps-fintiri-winner-of-adamawa-governorship-election.html