Aisha Dahiru Ahmad
Aishatu Dahiru Ahmed, ( an haife ta a watan Augusta shekarata alif 1971) wacce aka fi sani da Binani, ‘yar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa. Tsohuwar Sanata ce data wakilci Adamawa ta tsakiya a majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin Tutar jam'iyyar APC mai alamar tsintsiya. Sa'annan tayi takarar gwamna a shekarar 2023 ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC.
Aisha Dahiru Ahmad | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - ← Aisha Dahiru Ahmad - Abbas Aminu Iya (en) → District: Adamawa Central
6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015 District: Yola North/Yola South/Girei
3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007 | |||||||
Rayuwa | |||||||
Cikakken suna | Aishatu Dahiru Ahmed | ||||||
Haihuwa | Jahar Kaduna, 11 ga Augusta, 1971 (53 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
University of Southampton (en) Jami'ar Jihar Nasarawa | ||||||
Harsuna |
Turanci Fillanci Hausa | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa da injiniyan lantarki | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa |
Peoples Democratic Party All Progressives Congress |
Farkon Rayuwa
gyara sasheAn haifi Aisha a ranar 11 ga watan Agusta, shekara ta alif ɗari tara da saba'in da ɗaya 1971A.c. Ta taba zama ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a matsayin mamba a jam’iyyar People’s Democratic Party tsakanin shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.
Karatu
gyara sasheAisha Binani ta yi karatun firamare da sakandare a jihar Kaduna kafin ta wuce Jami’ar Southampton, inda ta samu digiri na uku a fannin Eleteical Engineering.[1]
AIki
gyara sasheBinani ta kafa kamfanin Binani Nigeria Limited, ƙungiyar Binani Group of Companies da nufin bunkasa da inganta tattalin arziƙin yankin Arewa maso Gabasa a ƙasar Najeriya.
SIYASA
gyara sasheTa shiga harkar siyasa ne a shekarar 2011 lokacin da aka zaɓe ta a matsayin ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya Daga jihar, Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Daga baya ta sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ta tsaya takarar Sanata inda ta lashe zaɓen kujerar a matsayin sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya. A matsayinta na yar majalisar dattijai, Binani ta yi aiki a matsayin shugabar kwamitin majalisar dattawa kan manufofin ci gaba mai dorewa (SDGs).[2]
Takarar Gwamna
gyara sasheSanata Aisha Dahiru Ahmed Binani ta lashe tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Adamawa inda ta doke maza shida da kuma jiga-jigan siyasar Jihar Adamawa.
A zaɓen fidda gwanin dai, Binani ta samu kuri’u 430, wanda ya zama mafi rinjaye a zaɓen, inda ta doke Nuhu Ribadu,[3] tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Action Congress kuma Tsohon shugaban hukumar Yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC na farko, wanda ya samu ƙuri’u 288. Muhammadu Jibrilla Bindow, gwamna mai barin gado ya zo na uku da ƙuri’u 103, Abdurrazaq Namda ya zo na biyu da ƙuri’u 94 sai Wafari Theman da 39. Wafarniyi Theman da Umar Mustapha Madawaki ne suka samu matsayi na biyar da shida a zaben fidda gwanin.[4] A ranar 14 ga Oktoba, 2022, wata babbar kotun tarayya da ke Yola ta soke takarar Binani a matsayin yar takarar gwamnan Jihar Adamawa ta jam’iyyar APC.[5]
Hukuncin da kotun ta yanke, ta bayyana cewa babu dan takarar jam’iyyar APC a jihar a zaben 2023 amma ta ce masu kara da wadanda ake kara suna da damar daukaka kara kan hukuncin.[6] Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa.
Mista Fintiri ya lashe zaben cike gurbin da kuri'u 9,337. Ya kayar da babbar abokiyar hamayyar sa, Aisha Dahiru, wanda aka fi sani da Binani, ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ta zo ta biyu a zaben da kuri’u 6,513.[7]
A babban zaben da aka gudanar da kuma zaben da aka sake Fintiri na Jam'iyyar PDP ya samu kuri’u 430,861 yayin da yar takarar APC ta samu kuri’u 398,788.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.shineyoureye.org/person/aishatu-dahiru-binnan
- ↑ https://hausa.leadership.ng/tikitin-tsayawa-takarar-aisha-binani-ya-karfafa-siyasar-matan-arewa/
- ↑ https://www.thecable.ng/history-as-aishatu-binani-beats-ribadu-bindow-to-adamawa-apc-guber-ticket/amp/
- ↑ https://dailytrust.com/seven-things-to-know-about-aisha-binani/
- ↑ https://www.google.com/amp/s/www.bbc.com/hausa/articles/cndrdjgegj8o.amp
- ↑ https://www.bbc.com/pidgin/articles/czq3dg723ewo
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/594019-updated-inec-declares-pdps-fintiri-winner-of-adamawa-governorship-election.html