Aisha Tsamiya

Ƴar'wasan fim ɗin Kannywood a Najeriya
(an turo daga Aisha Aliyu Tsamiya)

Aisha Aliyu Tsamiya Wacce akafi sani da A'isha Tsamiya ta kasance jaruma a masana'antar funafinai ta Hausa kannywood. Ta yi fina- finai da dama irin su Ɗakin Amarya, Rayuwa Bayan mutuwa, Aisha Tsamiya bayan tayi dogon zango a masana'antar sai kwatsam aka ji za ta yi aure.

Aisha Tsamiya
Rayuwa
Haihuwa Nasarawa, 1992 (31/32 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Yusuf Maitama Sule Un AUWALI SANI BENA (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a jarumi

Manazarta

gyara sashe

(An haife ta a shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da cassa'in da biyu 1992A.C) Miladiyya . a ƙaramar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano a Arewacin Nijeriya. Tayi karatunta na firamare da sakandare a Giginyu. Sannan jarumar tayi karatunta a Jami'ar Yusuf Maitama Sule dake jihar Kano.[1] [2]A halin yanzu Aisha tsamiya tana cigaba da Neman ilimi domin ƙara habaka aikinta na shirya finafinai. Aisha Tsamiya tayi aure tare da mijin nata mai suna Alhaji Abubakar Buba a ranar 26/02/2022, sannan mijinta yakasance ɗan kasuwa kuma ɗaya daga cikin jigajigan Yan siyasar jahar yobe kuma ɗaya daga cikin na Hannun daman Gwamnan jihar Mai Mala Buni. A yanzu dai tana da shagon da ta buɗe na siyar da mayamayen gyaran fata kuma tana koyar da girke girme a shafinta na Tiktok.

Fina finan ta

1 Dakin amarya

2 Abba na

3 Tafin hannu

4 Jamila

5 Zinat

6 zarge

7 manyan mata da sauran su.

Aisha Aliyu, wata matashiyar ƴar fim ɗin Hausace da take da burin zama babba a harkar fim. An kuma haifeta a ƙaramar hukumar Nasarawa dake jihar Kano. Tayi makarantar firamare da sakandare ta Giginyu kuma a halin yanzu tana kan cigaba da karatun ta ne tanada burin yin karatu mai zurfi.

Ta fara aiki ne a matsayin mai ɗaukar nauyin fim ɗin ta da kanta saboda sha'awar fina-finai don isar da sako ga al'ummarta, saƙonni kan canjin zamantakewa. Fim dinta na farko shi ne Tsamiya daga nan sai wani fim mai suna Rabi’a, Rayuwa Bayan Mutuwa, Uzuri da Dakin Amarya. Hakika Aisha Tsamiya ta nuna wa duniya ita ba kanwar lasa ba ce, domin har yanzu tana ci gaba da bayyanar da hazaka da kwarewarta a fagen finafinan Hausa. Tsamiya ta zama ɗaya daga cikin fitattun ƴan fim goma a cikin jaruman Kannywood a shekara ta 2016.[3] Hakanan Kuma Tsamiya na da masoya da mabiya masu ɗimbin yawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo.[4][5]

Aisha Aliyu tsamiya matashiyar 'yar fim ce data nuna bata da sha'awar shiga masana'antar da shirya fina finan hausa.

An haifi Aisha tsamiya a shekara ta dubu ɗaya da darin tara da cassa'in da biyu 1992 a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano, ta tafi makarantar firamare ta Giginyu sannan ta halarci makarantar sakandire.

Fina-Finai

gyara sashe

Ga jerin fina-finai da Aisha Aliyu (Tsamiya) ta ksance a ciki:

  • Tsamiya
  • Ranar Baiko
  • Hanyar Kano
  • Bahaushiya
  • Da Kishiyar Gida
  • Dakin Amarya
  • Husna
  • Jamila
  • Mai Dalilin Aure (Match Maker)
  • Makahon Gida
  • Munubiya
  • Niqab
  • Nisan Kiwo
  • Rayuwa Bayan Mutuwa
  • Zeenat
  • Kalan Dangi
  • Mijin biza
  • Abbana
  • Tafin hannu
  • salma
  • Manyan mata
  • Burin fatima
  • Dawo dawo
  • Mar'atussaliha

Aisha Tsamiya ta fara aiki ne saboda sha'awar da takeyiwa sana'ar shirya fina-finan Hausa a cewar ta domin isar da sako ga al'umma. Film din Tsamiya shine film din data fara suna a cikin shi, sannan ta fito a film din Rayuwa bayan Mutuwa, Uzuri, Dakin Amarya, kalan dangi da dai sauran su.

Aisha tsamiya ta zama matsayi na goma a shahararren film ɗin salma, hakika har yanzun Aisha tsamiya tana daga cikin matan da tauraruwar su ta dade tana haskawa a masana'antar shirya fim na hausa, kuma ta kware sosai a wannan sana'ar ta shirya fina finan hausa.sannan tazamo ɗaya daga cikin jaruman da ake mutumtawa saboda Bata shigar banza, ba,a taba ganinta da shigar da Bata dace ba ga addininta .Aisha tsamiya mace ce me natsuwa da Kamala da mutunci acikin jerin jaruman kanniwud watau masana,antar shirya fina finai na Hausa.

A halin yanzu dai Aisha tsamiya tana cigaba da neman ilimi a arewa. Aisha tsamiya har yanzun jarumar tayi aure a shekarar dubu biyu da Ashirun da biyu (2022) Alu,mma da dama sun mata fatan alkhairi domin tanada masoya masu yawa kasancewarta jarumar da ake ganin mutuncinta a masana,antar kanniwud, A halin yanzun jarumar tana sana,a inda tabude shagon Abaya dogayan riguna na mat, sannan tana koyar da girke girken zamani a shafinta na TikTok.

Manazarta

gyara sashe