Abubakar Momoh
Abubakar Momoh ɗan siyasan Najeriya ne kuma injiniya. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa shi minista a hukumar raya Neja Delta. Ya kasance tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Edo kuma tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Etsako, a jihar Edo. [1]
Abubakar Momoh | |||
---|---|---|---|
3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007 - Johnson Oghuma (en) → District: Etsako East/Etsako West/Etsako Central | |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yaren afenmai | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci pidgin Yaren afenmai | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAbubakar daga. Imiegba, North Ibie, Etsako East LGA of Edo State yake. Ya kammala karatunsa a jami'ar Benin inda ya karanci ilimin kimiyyar sinadarai. Ya kuma sami digiri na biyu a fannin injiniyan sinadarai daga Jami'ar Legas da kuma digiri na biyu a fannin harkokin gwamnati daga Jami'ar Ambrose Ali da ke Ekpoma.
Shi ma'aikaci ne a Cibiyar Gudanar da Harkokin Jama'a (FPA) kuma memba ne mai rijista a kungiyar Injiniya ta Najeriya da kuma Majalisar Dokokin Injiniya a Najeriya (COREN).
Aikin siyasa
gyara sasheAbubakar Momoh ya fara siyasa ne a matsayin kansila zuwa shugaban ƙaramar hukuma. A shekarar 1999-2003 ya zama ɗan majalisa a majalisar dokokin jihar Edo kafin ya je tarayya ya yi aiki a mazaɓar tarayya ta Etsako tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007. An kuma zaɓe shi a karo na biyu a matsayin ɗan majalisar wakilai tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015. Ya sauya sheka a shekarar 2019 ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) don neman kujerar Sanatan Edo ta Arewa amma ya faɗi zaɓe. Daga baya ya koma jam’iyyarsa ta APC. A shekarar 2023, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Abubakar Momoh a matsayin ministan raya yankin Neja Delta. [2] [3] [4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Akintayo, Kabir (2023-08-17). "Tinubu Appoints 62-year-old Abubakar Momoh as Youth Minister". Politics Digest (in Turanci). Retrieved 2023-10-27.
- ↑ Effiong, Sarah (2023-08-30). "Abubakkar Momoh; biography, education, career and politics". platinumtimes.ng (in Turanci). Retrieved 2023-10-27.
- ↑ Akintayo, Kabir (2023-08-17). "Tinubu Appoints 62-year-old Abubakar Momoh as Youth Minister". Politics Digest (in Turanci). Retrieved 2023-10-27.
- ↑ "Tinubu Brings Back Niger Delta Development Ministry, Names Momoh Minister-designate – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2023-10-27.