Abdulkadir Rahis
Abdulkadir Rahis (an haife shi a ranar 30 ga watan Yuni 1968) [1] ɗan siyasan Najeriya ne a halin yanzu yana aiki a matsayin ɗan majalisar wakilai ta Najeriya mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Maiduguri (Birnin) a majalisar wakilai ta ƙasa ta 10. Ɗan jam’iyyar APC ne kuma ya yi wa’adi uku a majalisar wakilai. [2]
Abdulkadir Rahis | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - District: Maiduguri (Metropolitan)
ga Yuni, 2015 -
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Maiduguri (en) , 30 ga Yuni, 1968 (56 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||
Karatu | |||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Tarihi da farkon rayuwarsa
gyara sasheAbdukadir ya yi karatu a kwalejin kimiyya da fasaha ta ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno, kuma ya kammala a shekarar 1989.[3]
Aikin siyasa
gyara sasheRahis ya fara harkar siyasa ne a shekarar 1990, lokacin da ya tsaya takarar kansila a shiyyar Shehuri ta Kudu da ke Maiduguri Metropolitan Council. A shekarar 1997 aka zaɓe shi shugaban Ward a ƙarƙashin jam'iyyar United Nigeria Democratic Party sannan a shekarar 1999 ya zama ma'ajin jam'iyyar All People's Party a Maiduguri Metropolitan Council.[3]
A cikin shekara ta 2001, an naɗa shi a matsayin Kansilan Kula da Ayyuka a Majalisar Dokokin Maiduguri, aikin da ya yi har zuwa shekara ta 2003. A shekarar 2003, an naɗa shi mamba a kungiyar kwallon kafa ta El-Kanemi Warriors, sannan ya zama shugaban hukumar. Ya kuma riƙe muƙamin shugaban matasan jihar Borno daga shekarun 2006 zuwa 2011 kafin Gwamna Kashim Shettima ya naɗa shi mataimaki na musamman. A cikin shekara ta 2012, an naɗa shi a matsayin Shugaban Kwamitin Riƙo na Maiduguri Metropolitan Council kuma ya yi aiki har zuwa shekara ta 2015.[3]
A shekarar 2015, an zaɓe shi a matsayin mamba mai wakiltar Maiduguri Metropolitan Federal Constituency na jihar Borno a majalisar wakilai, a ƙarƙashin jam'iyyar APC.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 9 December 2024.
- ↑ "10th National Assembly Members". Orderpaper.ng. Retrieved 9 December 2024.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 Maitela, Muhammad. "Hon. Abdulkadir Rahis is committed to representing the community well". Hausa leadership.ng.
- ↑ Hussaini, Hayatu (January 5, 2021). "Hon. Abdulkadir Rahis: Borno lawmaker with a difference". Blueprint Newspapers Limited.