Abdulaziz Usman
Abdulaziz Usman Tarabu (An haife shi a ranar 1 ga watan janairu, a shekara ta alif 1962) ɗan majalisar dattawan Najeriya ne mai wakiltar jam'iyyar PDP a jihar Jigawa. Ya zama dan majalisar dattawan Najeriya a shekarar 2007.[1]
Abdulaziz Usman | |||||
---|---|---|---|---|---|
ga Yuni, 2011 - ga Yuni, 2015 District: Jigawa North-East
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 District: Jigawa North-East | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 1 ga Janairu, 1962 (62 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Hausawa | ||||
Harshen uwa | Hausa | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Ilimi
gyara sasheAbdulaziz Usman yana da digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci.[2] Kafin shiga siyasa, ya kasance babban jami’in tsare-tsare a harkar noma da raya karkara ta Jihar Jigawa. An zabe shi a matsayin memba na Majalisar Wakilai daga shekara ta alif 1999 zuwa shekarar, 2003, kuma an sake zaɓe shi a shekarar, 2003-zuwa shekarar 2007.[1]
A shekarar, 2005, ya goyi bayan Atiku Abubakar, wanda shine mataimakin shugaban kasar Najeriya a lokacin, a wani zargin batanci ga mujallar Newswatch da ke da alaka da zargin cin hanci da rashawa, a lokacin da Atiku ke shugabantar majalisar zartarwa ta kasa.[3]
Aikin majalisar dattawa
gyara sasheAn zabi Abdulaziz Usman ɗan majalisar dattawa ta ƙasa mai wakiltar mazaɓar Jigawa ta arewa maso gabas a shekarar, 2007.[1] Wani rahoto da jaridar This Day ta fitar a watan Mayun na shekarar, 2009 ya ce bai dauki nauyin wani kudiri ba, duk da cewa yana daukar nauyin wasu kudirori, wani lokacin kuma yana ba da gudummawa wajen muhawara a zauren majalisar. Ya kasance shugaban kwamitin kula da harkokin majalisar dokoki.[4][5] A zaben watan Afrilun shekara ta, 2011 ya sake zabensa a matsayin Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Gabas a jam'iyyar PDP, da kuri'u, 135,202.[6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 https://web.archive.org/web/20160303170735/http://www.nassnig.org/senate/member.php?senator=73&page=1&state=19
- ↑ http://www.nigeriansenate.org/thesenator.php?%20NAME=ausman@nigeriansenate.org[permanent dead link]
- ↑ https://web.archive.org/web/20110727104430/http://www.newswatchngr.com/editorial/allaccess/nigeria/10926142113.htm
- ↑ https://allafrica.com/stories/200905250350.html?page=3
- ↑ https://web.archive.org/web/20110708221443/http://sunday.dailytrust.com/index.php?option=com_content&view=article&id=640%3Awhy-are-they-in-the-senate&catid=57%3Acover&Itemid=126
- ↑ https://allafrica.com/stories/201104111801.html