Abdulazeez Ibrahim
Abdulazeez Abubakar Ibrahim (27 Nuwamba 1957[1] – 5 Oktoba 2021)[2] an zaɓe shi ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Taraba ta tsakiya a jihar Taraba, Najeriya a farkon jamhuriya ta huɗu ta Najeriya, yana takara a ƙarƙashin jam'iyyar People's Democratic Party (PDP). Ya hau mulki a ranar 29 ga Mayun shekarar 1999.[3] An sake zaɓen shi a cikin Afrilun shekarar 2003.[4]
Abdulazeez Ibrahim | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Bangare na | Nigerian senators of the 4th National Assembly (en) da Nigerian senators of the 5th National Assembly (en) |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Sunan asali | Abdulazeez Ibrahim |
Suna | Abdelaziz |
Sunan dangi | Ibrahim |
Shekarun haihuwa | 27 Nuwamba, 1957 |
Wurin haihuwa | Jahar Taraba |
Lokacin mutuwa | 5 Oktoba 2021 |
Yaren haihuwa | Hausa |
Harsuna | Turanci, Hausa da Pidgin na Najeriya |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | mamba a majalisar dattijai ta Najeriya |
Ilimi a | Jami'ar Ahmadu Bello |
Ɗan bangaren siyasa | Peoples Democratic Party |
Ƙabila | Hausawa |
Fage
gyara sasheAn haifi Ibrahim a shekarar 1957. Ya yi digirin digirgir a fannin Injiniya da harkokin kasuwanci a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.[5]
Sana'ar siyasa
gyara sasheBayan ya hau kujerarsa a Majalisar Dattawa a watan Yunin shekarata 1999 an naɗa shi kwamitocin kasuwanci (mataimakin shugaban ƙasa), masana'antu, sufurin jiragen sama, Kimiyya da Fasaha, Wutar Lantarki da Ƙarfe, Tsarin Ƙasa da Ayyuka na Musamman.[6] A watan Afrilun 2005 yana cikin wasu Sanatoci da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka (ICPC) ta yi wa tambayoyi game da badaƙalar da aka ce Ministan Ilimi Fabian Osuji ya biya Naira miliyan 55 na cin hanci da rashawa don haka za su yi wa ƙasafin kuɗin ma’aikatar zagon-kasa.[7] A zaɓen da aka yi a watan Afrilun 2007 ya kasance ɗan takarar gwamnan jihar Taraba da ya tsaya takara a jam'iyyar All Nigeria People's Party (ANPP).[8] Ɗanbaba Suntai na PDP ne ya lashe zaɓen.[9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://books.google.com.ng/books?id=x6Q-AQAAIAAJ&q=Abubakar+Abdulazeez+Ibrahim+November+27+,+1957&redir_esc=y
- ↑ https://sunnewsonline.com/breakingsenator-ibrahim-is-dead/
- ↑ http://psephos.adam-carr.net/countries/n/nigeria/nigerialeg2.txt
- ↑ https://web.archive.org/web/20100720021846/http://www.dawodu.com/senator.htm
- ↑ https://web.archive.org/web/20220204124255/https://www.nigerianmuse.com/
- ↑ https://web.archive.org/web/20091118151316/http://www.nigeriacongress.org/assembly/committees1.htm
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-09. Retrieved 2023-03-09.
- ↑ https://afripol.org/DNA.htm[permanent dead link]
- ↑ http://nggovernorsforum.org/index.php?option=com_content&task=view&id=55&Itemid=