Zaɓen Gwamnan jihar Yobe na shekarar 2019

Zaben gwamnan jihar Yobe na 2019 ya gudana a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2019, dan takarar APC Mai Mala Buni ne ya lashe zaben, inda ya kayar da Umar Iliya Damagum na PDP.

Infotaula d'esdevenimentZaɓen Gwamnan jihar Yobe na shekarar 2019

Iri gubernatorial election (en) Fassara
Kwanan watan 9 ga Maris, 2019
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara Jihar Yobe
Zaben 2019

Mai Mala Buni ya zama dan takarar gwamna na APC bayan ya samu kuri’u 2,797 sannan ya kayar da babban abokin karawarsa, Honorabul Sidi Karasuwa wanda ya samu kuri’u 23. Inda ya zabi Alhaji Idi Barde Gubana a matsayin mataimakin sa. Umar Iliya Damagum shi ne dan takarar PDP tare da Baba Abba Aji a matsayin abokin mataimakin sa. ‘Yan takara 13 ne suka fafata a zaben.

Tsarin zabe gyara sashe

An zabi Buni a matsayin Gwamnan jihar Yobe ta hanyar amfani da tsarin kada kuri'a .

Zaben Fidda Gwani gyara sashe

Fidda gwanin APC gyara sashe

Zaben fidda gwani na APC a karon farko, ya gudana ne a ranar 30 ga watan Satumba, 2018. Mai Mala Buni ya lashe zaben fidda gwanin inda ya samu kuri’u 2,797 inda ya kara kuma ya kayar da wasu ‘yan takara 3. Babban abokin hamayyarsa shi ne Sidi Karasuwa, wanda ya zo na biyu da kuri’u 23, Umar Ali ya zo na uku da kuri’u 8, yayin da Aji Kolo ya samu kuri’u 4.

'Yan takara gyara sashe

  • Dan takarar jam’iyya: Mai Mala Buni
  • Mataimaki: Idi Barde Gubana
  • Sidi Karasuwa
  • Aji Kolo

Zaben fidda gwani na PDP gyara sashe

An gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP a ranar 30 ga watan Satumba, 2018. Umar Iliya Damagum ya fito ne a matsayin dan takarar hadin kai bayan da babban abokin hamayyarsa Umar Elgash Maina ya janye.

'Yan takara gyara sashe

  • Dan takarar jam’iyya: Umar Iliya Damagum
  • Abokiyar takara: Baba Abba Aji
  • Umar Elgash Maina- ya janye

Sakamako gyara sashe

Kimanin ‘yan takara 13 ne suka yi rijista tare da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa don tsayawa takara a zaben.

Adadin wadanda suka yi rijista a jihar don jefa kuri'a ya kai 1,365,913, yayin da aka tantance 546,391. Adadin kuri'un da aka kada sun kasance 560,492, yayin da ingantattun kuri'u suka kasance 546,391. Kuri’un da aka ki amincewa da su kuwa yawansu ya kai 14,101.Template:Election results

Ta karamar hukuma gyara sashe

Ga sakamakon zaben da karamar hukumar ta yi wa manyan jam’iyyun biyu. Jimillar halastattun kididdigar kuri'u 546,391 da aka kada ga wakilan jam'iyyun siyasa 13 da suka tsaya takara. Shudi yana nuni da kananan hukumomi wadanda Mai Mala Buni ya ci. Kore yana nuni da kananan hukumomi wadanda Umar Iliya Damagum ya ci.

LGA Mai Mala Buni

APC

Umar Iliya Damagum

PDP

Jimlar Kuri'u
# % # % #
Damaturu 26,087 3,760
Geidam 18,724 2,760
Nguru 28,366 19,468
Bade 32,213 8,854
Yunusari 28,858 893
Karasuwa 24,262 2,762
Yusufari 22,221 2,964
Potiskum 54,773 5,114
Fune 36,040 14,327
Jakusko 30,828 5,887
Bursari 20,657 2,813
Gulani 21,765 4,576
Fika 36,519 9,552
Machina 16,950 2,164
Nangere 25,698 4,765
Tarmuwa 11,338 3,925
Gujba 17,714 1,119
Alsidaya 444,013 95,703 546,391

Manazarta gyara sashe