Yetunde Onanuga
Yetunde Onanuga (an haife ta 11 Satumba 1960) ƴar siyasan Nijeriya ce wanda ta kasance mataimakiyar gwamnan jihar Ogun .
![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ibadan, 11 Satumba 1960 (60 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
ƙungiyar ƙabila | Yarbawa |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Makaranta |
Olabisi Onabanjo University (en) ![]() |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
RayuwaGyara
An haifi Onanuga a asibitin Adeoyo da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo a Najeriya. Mahaifinta shine FT Fabamwo.[1]
Ta yi karatu a jihar Ogun sannan kuma a Legas inda ta samu shaidar malanta. Daga baya ta kammala MBA a Jami'ar Jihar Ogun .
Tana aiki a ma'aikatar kula da muhalli ta jihar Legas lokacin da aka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar Ibikunle Amosun a 2015. Amosun shi ne ɗan takarar da ke kan kujerar amma mataimakinsa na baya ya koma jam'iyyar adawa. Amosun ya zaɓi Onanuga daga cikin mutane uku masu yuwuwar tsayawa takara. [2]
An zaɓi Onanuga mataimakiyar gwamna. [3]
BayaniGyara
- ↑ Onanuga: Round peg in round hole, 7 January 2015, The Nation Online NG, Retrieved 17 February 2016
- ↑ How Amosun’s running mate emerged, 19 December 2014, VanguardNGR, Retrieved 17 February 2016
- ↑ HID Awolowo passes on at 99, 2015, ThisDayLive, Retrieved 18 February 2016