Yaou Aïssatou
Yaou Aïssatou (an haife ta a ranar 28 ga watan Nuwamba 1951) ita ce Darakta Janar na Kamfanin Zuba Jari na Ƙasar Kamaru (NIS). Ta kasance ministar harkokin mata ta farko a Kamaru.[1]
Yaou Aïssatou | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Tcheboa (en) , 28 Nuwamba, 1951 (72 shekaru) |
ƙasa | Kameru |
Karatu | |
Makaranta |
University of Rouen (en) Georgetown University (en) Claremont Graduate University (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Mai tattala arziki, ɗan siyasa, Mai kare ƴancin ɗan'adam da ɗan kasuwa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Cameroon People's Democratic Movement (en) |
Rayuwar farko
gyara sasheAïssatou ɗiyar lamido ce ta Tchéboa a yankin Arewa ta Kamaru, inda ta yi makarantar sakandare. Ta ci gaba zuwa Lycée Technique a Douala, inda ta sami digiri a cikin shekarar 1971. Bayan kammala karatunta ta yi karatu a fannin tattalin arziki a Jami'ar Rouen da ke Faransa, inda ta sami digiri na BA a shekarar 1975. Ta yi aiki tare da NIS a Kamaru na ɗan gajeren lokaci kafin ta tafi Amurka don yin karatu a Jami'ar Georgetown da Claremont Graduate School, ta kammala karatun MBA. [2]
Sana'a
gyara sasheDa ta koma Kamaru a shekarar 1979 ta koma NIS a matsayin mataimakiyar daraktar kuɗi. A watan Fabrairun 1984 aka ba ta muƙamin minista na farko a matsayin ministar harkokin mata ta Kamaru. Ta maye gurbin Delphine Zanga Tsogo a cikin watan Maris 1985 a matsayin shugabar ofishin ƙasa na kungiyar Mata ta Jam'iyyar Dimokuraɗiyyar Jama'ar Kamaru mai mulki, kuma an kara mata girma a watan Mayu 1988 zuwa matsayin ministar zamantakewa da harkokin mata, tana aiki har zuwa Afrilu 2000. [3] A shekara ta 2009 ne aka naɗa ta bisa umarnin shugaban ƙasa a matsayin sabuwar shugabar hukumar ta NIS, inda ta maye gurbin Esther Dang Belibi wacce ta yi murabus a cikin wata takaddama. [4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ DeLancey, Mark Dike; Mbuh, Rebecca; DeLancey, Mark W. (2010). Historical Dictionary of the Republic of Cameroon. Scarecrow Press. pp. 46–7. ISBN 978-0-8108-7399-5.
- ↑ Ngogang, Thierry. "Nomination: Yaou Aissatou rebondit à la Sni". Cameroon-Info.Net. Retrieved 16 November 2016.
- ↑ Foute, Rousseau-Joël. "SNI: les ambitions de Yaou Aïssatou". Cameroon-Info.Net. Retrieved 16 November 2016.
- ↑ "Esther Dang: La démission qui fait du bruit". Journal du Cameroun (in Faransanci). 2010-02-15. Retrieved 2021-01-28.