Umar Gombe
Umar Sani Labaran, Wanda aka fi sani da Umar Gombe (An haife shi a ranar 5 ga watan Afrilu, shekarata 1983) a Gombe, Jihar Gombe, a Najeriya. ɗan wasan kwaikwayo ne na Najeriya, mai shirya fina-finai, kuma darakta.[1] Wanda ya fito a fina-finai sama da ɗari. Umar Gombe ya kasance manajan shirye-shirye na farko da ake watsawa a tashar Northflix.[2] Baya ga fitowa a fina-finai, yana kuma fitowa a shirye-shiryen talabijin, rediyo, da kuma wasannin barkwanci. Sau da yawa an zaɓe shi a matsayin gwarzon ɗan wasan kwaikwayo, kuma ya lashe wasu kyaututtuka da dama.
Umar Gombe | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Umar Sani Labaran |
Haihuwa | 13 ga Afirilu, 1983 (41 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
IMDb | nm13173654 |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Umar Gombe ga iyalan Kano ranar 5 ga watan Afrilu, shekara ta 1983 a Gombe, Najeriya. Dan Malam Sani Labaran ne, manomi, dattijo kuma mamba a kungiyar tuntuɓa ta Arewa.
Daga shekara ta 1986 zuwa 1998, yayi karatu a makarantun gandun daji, firamare, da sakandare a jihar Gombe, da jihar Bauchi. Ya ci gaba da karatunsa a Jami’ar Bayero Kano, inda ya samu shaidar difloma a fannin harkokin gwamnati da sarrafa bayanai da fasahar sadarwa (diplomas in Public Administration and Data Processing & Information Technology).[3] Umar yana da digiri na farko a fannin fasahar sadarwa da tsarin bayanan kasuwanci daga Jami'ar Middlesex Dubai, kuma a halin yanzu yana karatun MBA a Jami'ar (National open University) ta Najeriya.[4]
A shekara ta 2014, Umar Gombe ya halarci wani shirin horar da fina-finai a Cibiyar Nazarin Fina-Finai da Talabijin ta Asiya, Noida a Indiya, shirin da Majalisar Dinkin Duniya ta aiwatar[5], tare da sauran jaruman Kannywood da suka halarci ci taron kamar su Falalu A Dorayi, Ali Nuhu, Ishaq Sidi Ishaq da kuma Ibrahim. Mandawari.
Muƙami da Aikin fim
gyara sasheAn naɗa Umar Sani Labaran a matsayin shugaban riko na kungiyar masu yin Hotunan Hot ta Najeriya a shekara ta 2021,[6] sannan ya zama mataimakin sakataren kungiyar na kasa bayan zaɓen da akayi a shekera ta 2022.
Umar ya fara fitowa a fina-finan Hausa a shekara ta 2001 a wani fim mai suna Shaida, wanda ya taimaka masa ya yi suna da kuma samun karbuwa a wajen jama’a da dama a masana’antar, daga karshe ya zama jigo a fina-finan Fasaha kafin ya koma ISI Films, wanda fitaccen jarumin fina-finai Ishaq Sidi Ishaq ya assasa, daga baya kuma kamfanin Kumbo Productions, ya shirya fim din Sanafahna, wanda ya yi fice a harkar fim. an ɗauki shirin fim ɗin a kasar Najeriya da Nijar. Ya fito a cikin fina-finan kamfanin Kumbo Productions da dama, da suka haɗa da Armala, Noor, da Sanafahna.[7]
A shekara ta 2014, ya fara fitowa a shirin wasan kwaikwayo na talabijin kuma mai dogon Zango Dadin Kowa[8] mallakin Arewa24, wanda ya samu lambar yabo. [14] A shekarar 2022, ya yi fice a karon farko a shirin mai dogon Zango na Gidan Badamasi [9] da ya samu lambar yabo, wani fim da ya shafi mata da maza don magance matsalolin zamantakewa wanda Faika Ibrahim Rahi ta bada umarni a fim ɗin, ta samu lambar yabo.[10]
Shahara
gyara sasheUmar Gombe ya yi fice ne bayan fitowa a fim din Nollywood na Turanci na Netflix, Tenant of the House,[11][12] wanda Kunle Afolayan da Adieu Salut suka shirya, da sauran fina-finan Hausa kamar Kwalla, Lambar Girma, Noor, Lissafi, Iko, da kuma In Zaki So Ni. Kuma ya taka rawar gani a fina-finai kamar Lissafi, Noor, Mati A Zazzau,[13] Kishiyata, Fati, Wakili, Hauwa Kulu, da ma jerin shirye-shiryen masu dogon Zango.
Umar ya tabbatar da kansa a matsayin ɗaya daga cikin jaruman Kannywood masu hazaka. Ya kuma taka rawar gani a cikin shirin Daɗin Kowa da ya samu lambar yabo,[14] wanda shi ne shirin fim mai dogon Zango na harshen Hausa na farko da aka fara nunawa a tashar Arewa24.[15] Umar kuma ya fito a cikin shirin mujallar iyali na Najeriya, Ongacious Zango na 2.
Fina-finai
gyara sasheDenotes films that have not yet been released |
Year | Title | Role | Genre | Note |
---|---|---|---|---|
2001 | Shaida | Actor | Drama | |
2001 | Haske | Actor | Drama | |
2002 | Duhun Damunai | Actor | Drama | |
2002 | Kwalla | Actor | Drama | |
2003 | Sansani | Actor | Drama | |
2004 | Ambaliya | Actor | Drama | |
2004 | Tutar So | Actor | Drama | |
2005 | Jarida | Actor | Drama | |
2006 | Takbir | Actor | Drama | |
2006 | Lada | Actor | Drama | |
2007 | Attajira | Actor | Drama | |
2007 | Nauyi | Actor | Drama | |
2008 | Iko | Actor | Drama | |
2008 | Budurwa | Actor | Drama | |
2008 | Jari Hujja | Actor/Writer | Drama | |
2009 | Wasila | Actor | Drama | |
2009 | Wasila (English) | Actor | Drama | |
2009 | Lissafi | Actor | Drama | |
2009 | Kusuwar Danga | Actor | Drama | |
2010 | Wa'azi | Actor | Drama | |
2010 | Bakar Ashana | Actor/Writer | Thriller | |
2010 | Fati | Actor | Drama | |
2010 | Sanafahna 2 | Actor | Drama | |
2010 | Ruwan Dare | Actor | Drama | |
2010 | Sauyin Lamari | Actor | Drama | |
2011 | Balele | Actor | Drama | |
2011 | In Zaki Soni | Actor | Drama | |
2011 | Noor | Actor/Producer | Drama | |
2014 | Aci Bulus | Actor | Drama | |
2014 | Armala[16] | Actor/Producer | Drama | |
2014 | Makuwa | Actor | Drama | |
2015 | Soyayaya Da Tsakuwa | Actor | Drama | |
2017 | Samari | Actor | Drama | |
2018 | Ni Da Kai Da Shi | Actor | Drama | |
2019 | Tenant Of The House | Actor | Drama | |
2019 | Gargadi[17] | Actor/Producer | Drama | Short film |
2020 | Mati A Zazzau[18] | Actor | Comedy/Drama | |
2021 | Hauwa Kulu | Actor | Drama | |
2021 | Wakili | Actor | Comedy/Drama | |
2021 | Ameer | Actor | Action/Drama | Short film |
2022 | Tsayin Daka | Actor | Drama | |
2022 | Maimunatu | Actor | Drama | |
2022 | Adieu Salut | Actor | SciFi |
Telebijin
gyara sasheYear | Title | Role | Genre | Notes |
---|---|---|---|---|
2014 | Dadin Kowa | Actor | Drama | Series regular (13 episodes)[19] |
2018 | Yan Birni (Makewayi) | Actor | Drama | A film powered by UNICEF |
2019 | Yan Zamani | Actor | Comedy/Drama | |
2021 | Gidan Danger | Actor | Drama | Series regular (13 episodes)[20] |
2021 | Bugun Zuciya | Actor | Drama | |
2021 | Yan Tagwaye | Producer | Drama | |
2022 | Gidan Badamasi | Actor | Comedy/Drama | Series regular (13 episodes)[21] |
2022 | Kishiyata | Actor | Drama | |
2022 | Sawun Giwa | Actor | Drama | |
2022 | Nasaba | Actor/Producer | Drama |
Murya
gyara sasheYear | Title | Role | Genre | Notes |
---|---|---|---|---|
2010 | Ruwan Dare | Actor | Drama | Ɗora muryar Jarumi |
2021 | Madubi | Actor | Drama | Ɗora muryar Jarumi |
Hanyoyin haɗin waje
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ Chidiebere Ihemebiri (2021-05-25). "I Found It Difficult Graduating From An Actor To A Producer – Umar Gombe". Daily Trust. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ Ibrahim Musa Giginyu (2022-04-19). "Kannywood Actor, Umar Gombe, Turns Pioneer Program Manager Of Northflix". Daily Trust. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ HausaFilms.TV (2018-07-12). "Umar Gombe HausaFilms.TV - Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities". HausaFilms.TV. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ Daily Trust (2021-05-21). "I would have become a model if I was not an actor - Umar Gombe - YouTube". Daily Trust. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ IFCPC (2018-05-12). "Indo Nigerian Film Association Moves Further Under ICMEI". IFCPC. Archived from the original on 2022-09-23. Retrieved 2022-09-23.
- ↑ Ahmed Lawal (2022-02-24). "Sarari appointed LOC chairman Zuma film festival". Bluprint. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ HausaFilms.TV. "Umar Gombe HausaFilms.TV - Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities". HausaFilms.TV. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ Arewa24. "Dadin Kowa - AREWA24". Arewa24. Retrieved 2022-09-16.
- ↑ Arewa24. "Gidan Badamasi - AREWA24". Arewa24. Retrieved 2022-09-16.
- ↑ Daily Trust. "Tambari by Daily Trust Tambari - Issuu". Daily Trust. Retrieved 2022-09-23.
- ↑ Netflix. "Watch Tenant of the House - Netflix". Netflix. Retrieved 2022-09-11.[permanent dead link]
- ↑ IMDb. "Tenant of the House (2019) - Full Cast & Crew - IMDb". IMDb. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ IMDb. "Mati a Zazzau (2020) - IMBd". IMDb. Retrieved 2022-09-17.
- ↑ BBC News Hausa (2021-10-21). "Daga Bakin Mai Ita Tare Da Umar Gombe - YouTube". BBC News Hausa. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ Arewa24 (2015-02-06). "DADIN KOWA EPS 3 PRT 1 - YouTube". Arewa24. Retrieved 2022-09-11.
- ↑ Flickr. "IMG_0709 - Producer/Actor Umar Gombe on set of Armala. - talatu-carmen - Flickr". talatu-carmen. Retrieved 2022-09-17.
- ↑ Mudari TV 24. "Gargadi - Warning! BY UMAR GOMBE - YouTube". Mudari TV 24. Retrieved 2022-09-17.
- ↑ IMDb. "Mati a Zazzau (2020) - IMBd". IMDb. Retrieved 2022-09-17.
- ↑ Arewa24. "Dadin Kowa - AREWA24". Arewa24. Retrieved 2022-09-16.
- ↑ Arewa24. "Gidan Danger Series - AREWA24". Arewa24. Archived from the original on 2022-09-20. Retrieved 2022-09-16.
- ↑ Arewa24. "Gidan Badamasi - AREWA24". Arewa24. Retrieved 2022-09-16.