Sheikh Mahmoud Khalil Abd al-Rahman al-Qari ya kasance limami a masallaci mai Alqiblah biyu da ke birnin madina kuma yayi limanci a masallacin manzon Allah a lokacin yana raye. Shi da ne a gurin Khalil Al-Qari.[1]

Sheikh Mahmoud Khalil Al-Qari
Rayuwa
Haihuwa Madinah
ƙasa Saudi Arebiya
Mutuwa Madinah, 25 ga Yuni, 2022
Makwanci Al-Baqi'
Ƴan uwa
Mahaifi Khalil Al-Qari
Ahali Mohamed Khalil Al-Qari (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Malamai Khalil Al-Qari
Sana'a
Sana'a qāriʾ (en) Fassara da Liman
Masallacin Madinah

Farkon rayuwa

gyara sashe

An haifi Mahmud Khalil Al-Qari kuma ya girma duk a Madina. Ya haddace Alqur'ani daga mahaifinsa Khalil Al-Qari, yana dan shekara goma. Ya kuma samu digirin farko a kwalejin Alqur’ani da Ilimin addinin Musulunci.

An ba da izinin sanya shi a matsayin Limamin Masallacin Annabi a Sallar Tarawihi a cikin watan Ramadan na shekara ta 1438AH da 1439 bayan hijira, wanda kuma ya yi dai-dai da shekarar milladiyya (2017 da 2018). Ya ci gaba da Limanci a masallacin Al-qiblatain har zuwa rasuwarsa.[2][3]

Ya rasu a safiyar ranar Asabar 26 ga watan Zul-Qa'dah 1443 AH daidai da 25 ga watan Yunin 2022 a Madina, a sashin kula da lafiya a wani asibiti bayan jinya. An yi Sallar Jana'izarsa a wannan rana bayan Sallar Magariba a Masallacin Annabi, an kuma binne shi a makabartar Al-Baqi.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "ما هو مرض الشيخ محمود خليل القارئ الذي تسبب بوفاته؟". 25 June 2022. Archived from the original on 1 July 2022. Retrieved 1 July 2022.
  2. "السعودية.. الموت يغيب الإمام السابق للمسجد النبوي". العربية. June 25, 2022. Archived from the original on July 1, 2022. Retrieved July 1, 2022.
  3. "وفاة إمام مسجد القبلتين في المدينة بعد وعكة صحية". 25 June 2022. Archived from the original on 2022-06-27.
  4. "Saudi Arabia.. Death misses the former imam of the Prophet's Mosque". 26 June 2022. Archived from the original on 2 July 2022. Retrieved 1 July 2022.