Shehu Abdullahi

Dan Wasan kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya


Shehu Usman Abdullahi (an haife shi a ranar 12 ga watan Maris 1993) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya wanda a halin yanzu yake taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Cyprus ta farko a ƙasar Omonia.

Shehu Abdullahi
Rayuwa
Haihuwa Jahar Nasarawa Sokoto, 12 ga Maris, 1993 (31 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Ƙungiyar kwallon kafa ta Maza ta Najeriya ta 'yan kasa da shekaru 202012-2013210
Kano Pillars Fc2012-2014
  Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya2014-
Qadsia SC (en) Fassara2014-201571
C.F. União (en) Fassara2015-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Lamban wasa 14
Nauyi 72 kg
Tsayi 178 cm
Shehu Abdullahi-Nigeria.jpg

Aikin kulob/ƙungiya

gyara sashe

Qadsiya SC

gyara sashe

A watan Yulin shekarar dubu biyu da goma sha huɗu, 2014, Abdullahi ya koma Kano Pillars, Nigeria, ya koma kungiyar Qadsia SC ta Kuwait, a kan kudi dala dubu ɗari huɗu da tamanin, $480,000, Abdullahi ya samu dala dubu ɗari uku da talatin, $330,000, sai Kano Pillars, kuɗi dala dubu ɗari da hamsin $150,000.

União da Madeira

gyara sashe

A ranar 6 ga watan Yunin shekarar dubu biyu da goma sha biyar 2015, Shehu ya koma sabuwar kungiyar Premier League ta CF União kan kwantiragin shekaru biyu.[1]

A ranar 2 ga watan Satumbar shekarar dubu biyu da goma sha shida 2016, Shehu ya koma kungiyar Anorthosis Famagusta ta ƙasar Cyprus kan yarjejeniyar shekara biyu kan kashi 20% [2] [3] na kudin sake siyar da 'yan wasan a wani kulob na Turai. [4]

A ranar 24 ga watan Janairun shekarar dubu biyu da goma sha takwas 2018, Shehu ya rattaɓa hannu kan ƙungiyar Bursaspor ta Turkiyya na tsawon shekaru biyu da rabi kan kuɗin da ba a bayyana ba.

A ranar 19 ga Satumbar shekarar dubu biyu da ashirin 2020, Shehu ya rattaɓa hannu a ƙungiyar ta Cyprus First Division Omonia .

Ayyukan kasa

gyara sashe
 
Shehu tare da Najeriya a 2017

A watan Janairun shekarar dubu biyu da goma sha huɗu 2014, babban kocin tawagar Stephen Keshi, ya gayyace shi zuwa cikin tawagar 'yan wasan kwallon kafa ta Najeriya a gasar cin kofin ƙasashen Afrika na 2014. Ya taimaka wa ƙungiyar zuwa matsayi na uku bayan Najeriya ta doke Zimbabwe da ci ɗaya mai ban haushi.

Najeriya ce ta zabe shi a cikin 'yan wasa 35 na wucin gadi a gasar Olympics ta bazara ta 2016.

A watan Mayun 2018 an saka shi cikin jerin ‘yan wasa 30 na farko da Najeriya za ta buga a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018 a Rasha.

Kididdigar sana'a

gyara sashe
As of 11 May 2021
Kulob Kaka Kungiyar Kofin kasa Kofin League Nahiyar Sauran Jimlar
Rarraba Aikace-aikace Buri Aikace-aikace Buri Aikace-aikace Buri Aikace-aikace Buri Aikace-aikace Buri Aikace-aikace Buri
União da Madeira 2015-16 Primeira Liga 28 1 1 0 1 0 - - 30 1
Anorthosis 2016-17 Sashen Farko na Cyprus 29 2 6 1 - - - 35 2
2017-18 19 1 2 0 - - - 21 1
Jimlar 48 3 8 1 - - - 56 4
Bursaspor 2017-18 Super Lig 14 0 - - - - 14 0
2018-19 13 1 - - - - 13 1
2019-20 1. Lig 33 4 0 0 - - - 33 4
Jimlar 60 5 0 0 - - - 60 5
Omonia 2020-21 Sashen Farko na Cyprus 30 0 1 0 - 4 0 - 35 0
Jimlar sana'a 166 9 10 1 1 0 4 0 0 0 181 10

Ƙasashen Duniya

gyara sashe
As of match played 16 July 2019[5]
Najeriya
Shekara Aikace-aikace Buri
2014 6 0
2015 4 0
2016 6 0
2017 6 0
2018 6 0
2019 3 0
Jimlar 31 0

Girmamawa

gyara sashe
  • Kofin Emir Kuwait : 2014–15
  • Kuwait Super Cup : 2014
  • AFC Cup : 2014

Omonia

  • Sashen Farko na Cyprus : 2020-21
  • Kofin Cyprus : 2021-22
  • Cypriot Super Cup : 2021

Ƙasashen Duniya

gyara sashe

Najeriya U23

  • Lambar tagulla a Wasannin Afirka : 2015

Tawagar Olympics ta Nigeria

  • Lambobin tagulla na bazara na Olympics : 2016

Manazarta

gyara sashe
  1. https://dailypost.ng/2015/07/30/siasia-danjuma-release-squad-lists-for-olympic-qualifiers/
  2. Διώχνει Κρέσπο, παίρνει Σεού και ελπίζει σε κάτι καλό μπροστά Archived 2017-02-15 at the Wayback Machine, themasport.com
  3. Ένας χάλκινος Ολυμπιονίκης στην Ανόρθωση (video) Archived 2018-04-30 at the Wayback Machine, reporter.com.cy
  4. Στην Ανόρθωση ο Abdullah Shehu, Anorthosis Famagusta Official Website
  5. "Shehu Abdullahi". National Football Teams. Benjamin Strack-Zimmerman. Retrieved 23 June 2018.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe