Shaista Suhrawardy Ikramullah
Begum Shaista Suhrawardy Ikramullah (22 ashirin da biyu ga watan Yuli shekara 1915 - zuwa sha daya ga watan 11 Disamba shekara 2000) yar [1] siyasan Bengal yar Pakistan ne daga Bengal, jami'in diflomasiyya kuma marubuci. Ita ce mace musulma ta farko da ta samu digirin digirgir a jami'ar Landan. Ta kasance jakadiyar Pakistan a Morocco daga shekara 1964 zuwa shekara 1967, kuma ta kasance wakiliya a Majalisar Dinkin Duniya.
Shaista Suhrawardy Ikramullah | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kolkata, 22 ga Yuli, 1915 |
ƙasa |
Pakistan British Raj (en) |
Harshen uwa | Urdu |
Mutuwa | Karachi, 11 Disamba 2000 |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Mohammed Ikramullah (en) |
Yara |
view
|
Karatu | |
Makaranta |
School of Oriental and African Studies, University of London (en) University of Calcutta (en) Loreto College (en) |
Harsuna | Urdu |
Sana'a | |
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya, ɗan siyasa da marubuci |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Jam'iyar siyasa | All India Muslim League (en) |
Iyali da ilimi
gyara sasheAn haifi Ikramullah a matsayin Shaista Akhtar Banu Suhrawardy cikin dangin Suhrawardy ga Hassan Suhrawardy da matarsa Sahibzadi Shah Banu Begum. Mahaifiyar Sahista ita ce jikanyar Nawab Abdul Latif.
Ta yi karatu a Loreto College, Kolkata. Ta kasance mace musulma ta farko da ta samu digirin digirgir a jami'ar Landan. Kundin karatunta na digirin digirgir, "Ci gaban Litattafan Urdu da Gajeren Labari", wani bincike ne mai mahimmanci na adabin Urdu.
Aure da yara
gyara sasheTa auri Mohammed Ikramullah a shekara ta 1933. Suna da 'ya'ya hudu:
- Imam Ikramullah
- Naz Ashraf
- Salma Sobhan
- Gimbiya Sarvath ta Jordan
Sana'ar siyasa
gyara sasheBayan aurenta, ta kasance daya daga cikin matan musulmin Indiya na farko da suka bar purdah a zamaninta. Muhammad Ali Jinnah ya zaburar da ita ta shiga harkar siyasa. [2] Ta kasance shugaba a kungiyar dalibai mata musulmi da kuma karamin kwamitin mata na kungiyar musulmi ta Indiya.[2]
A cikin shekara 1945, Gwamnatin Indiya ta nemi ta halarci taron dangantakar Pacific. Jinnah ya rarrashe ta da kin karbar wannan tayin, domin yana son ta je a matsayinta na wakiliyar kungiyar musulmi ta kuma yi magana a madadinta.
An zabe ta a Majalisar Wakilai ta Indiya a shekarar 1946, amma ba ta taba zama ba, kamar yadda 'yan siyasar kungiyar Musulmi ba su yi ba.
Ta kasance ɗaya daga cikin wakilai mata biyu a Majalisar Mazabar Mazabar Pakistan ta farko a shekara 1947. [3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ṣiddīqī, Muḥammad ʻAlī; Ikramullah, Shaista Suhrawardy (13 February 1997). Common Heritage. Oxford University Press. ISBN 9780195778083.
- ↑ 2.0 2.1 Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedSmith2008
- ↑ Begum Shaista Ikramullah storyofpakistan.com website, Retrieved 8 April 2019