Ahmad Babba Kaita
Ahmad Babba Kaita (An haifi Kaita ne a ranar 8, ga watan Satumba, shekarata 1968), kuma bahaushe ne.
Ahmad Babba Kaita | |||
---|---|---|---|
ga Yuni, 2019 - Mayu 2023 District: Katsina North | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Ahmad Babba Kaita | ||
Haihuwa | 1968 (55/56 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Congress for Progressive Change (en) |
Karatu da Aiki.
gyara sasheYa yi karatun firamari a Sada Primary School dake a Kankiya tsakanin 1974, zuwa 1980. Ya koyi karatun addini saga wurin mahaifinshi. Ya yi karatu a kwalejin Kufena Wusasa Zariya a jihar Kaduna tsakanin 1980, zuwa 1985. Ya yi karatun digiri na farko akan sociology a Bayero University dake Kano a 1992, bayan ya kammala sai yayin bautar kasa a jihar Fatakut a shekar 1994, zuwa 1995. Bayan ya kammala bautar kasa yayi aiki a Splendid International Limited, daya daga cikin kamfanonin mai da iskar a Najeriya, har na tsawon shekara 15, wanda ya kai matsayin manajin darakta. Ya kuma yi aiki a Everglades Agencies Limited kafin ya shiga siyasa [3 1]Ya kuma kasance mamba na Majalisar wakilan Najeriya, wanda ke wakiltar kwantuwansin Kankia/Ingawa/Kusada Jihar Katsina, Najeriya. Ya zama mamba ne a shekarar 2011.[2]
Manazarta.
gyara sashe- ↑ https://blerf.org/index.php/biography/babba-ahmad-kaita/
- ↑ "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". Nassnig.org. Retrieved 2020-01-08.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-09. Retrieved 2023-03-09.