Salifu Yakubu
Salifu Yakubu ɗan siyasan Ghana ne kuma jami’in diflomasiyya. Ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Savelugu daga shekara ta 1956 zuwa shekara ta 1966. Yayin da yake majalisar, ya ninka jakadan Ghana a Mali daga shekara ta 1961 zuwa shekara ta 1968.
Salifu Yakubu | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
9 ga Yuni, 1965 - 24 ga Faburairu, 1966 Election: 1965 Ghanaian parliamentary election (en)
1956 - 1965 Election: 1956 Gold Coast legislative election (en)
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Tamale, 15 Nuwamba, 1919 | ||||||
ƙasa | Ghana | ||||||
Mutuwa | 1968 | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
Achimota School Teachers' Training Certificate (en) : Craft Arts (en) Achimota School | ||||||
Harsuna | Turanci | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa da Malami | ||||||
Imani | |||||||
Addini |
Musulunci Musulmi |
Farkon rayuwa da aiki
gyara sasheYakubu yayi karatun sa na farko a makarantar gwamnati ta Tamale daga shekara ta 1929 zuwa shekara ta 1938. Ya cigaba a Kwalejin Achimota inda ya ci gaba da karatun kwasa-kwasan Fasaha da kere-kere, ya kammala a shekara ta 1940.
Ayyuka
gyara sasheYakubu ya shiga aikin koyarwa a makarantar Middle ta Tamale a shekara ta 1940 kuma ya koyar a can na shekara daya kafin ya shiga rundunar ‘yan sanda ta Gold Coast . Ya yi aiki a matsayin dan sanda ya hau mukamin sajan har sai da ya yi ritaya a ranar 12 ga Yulin shekara ta 1956.
Siyasa da nadin jakadanci
gyara sasheBayan yayi ritaya daga aikin ‘Yan Sanda, Yakubu ya tsunduma harkar siyasa. Ya tsaya takarar kujerar majalisar dokoki ta Savelugu kan tikitin Jam’iyyar Mutanen Arewa kuma ya yi nasara a shekara ta 1956. Ya cigaba da kasancewa memba na Jam’iyyar Mutanen Arewa har zuwa shekara ta 1958 lokacin da ya tsallaka katifu a majalisar ya shiga Jam’iyyar Taron Mutane .
A shekara ta 1961, aka naɗa Yakubu a matsayin jakadan Ghana a Mali . Ya yi aiki kuma a wannan matsayin har zuwa ɗaurin kurkuku a ranar 30 Disamban shekara ta 1968 kan laifuka biyu na almubazzaranci. Yayin da yake aiki a matsayin jakadan Ghana, Yakubu ya kasance dan majalisar na Savelugu har zuwa watan Fabrairun shekara ta 1966 lokacin da aka kifar da gwamnatin Nkrumah.[1][2][3][4][5][6][7]
Ya mutu a asibitin koyarwa na Tamale sakamakon rashin lafiya.
Duba kuma
gyara sashe- Ofishin jakadancin Ghana a Bamako
- Jerin sunayen MLA da aka zaba a cikin zaben majalisar dokoki na Gold Coast na shekara ta 1956
- Jerin 'yan majalisun da aka zaba a zaben' yan majalissun dokokin kasar Ghana a shekara ta 1965
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Debates, Part 2". Debates. Gold Coast Legislative Assembly: XV and xxxiii. 1956.
- ↑ "Parliamentary Debates; Official Report, Part 4". Ghana National Assembly. 1957: 254. Cite journal requires
|journal=
(help) - ↑ Daily Report, Foreign Radio Broadcasts, Issues 21–22 (Report). United States. Central Intelligence Agency. 1963. p. I 3.
- ↑ Steinburg, S. (27 December 2016). The Statesman's Year-Book 1962: The One-Volume ENCYCLOPAEDIA of all nations. p. 513. ISBN 9780230270916.
- ↑ "Africa Report, Volume 13". African-American Institute. 1968: 38. Cite journal requires
|journal=
(help) - ↑ "Parliamentary Debates; Official Report, Part 2". Parliamentary Debates. Ghana National Assembly: vi. 1965.
- ↑ Buser, Hans (2011). In Ghana at Independence: Stories of a Swiss Salesman. p. 20. ISBN 9783905758191.