Alhaji Saidu Umaru Namaska Ɗan Malam (An haifeshi ranar 31 ga watan Disamba, 1937 – Satumba 9, 2021) ya kasance cikin jerin sarakunan Najeriya na Sarautar gargajiya, Sarkin Kwantagora wanda yake da laƙabin Sarkin Sudan a Masarautar Kontagora. Mahaifinsa Umaru Sarkin Kudu ɗa ne ga Malam Umaru Nagwamatse wanda ya kafa Masarautar Kontagora kuma basarake daga Sakkwato. Ya rasu ne a ranar 9 ga watan Satumba, shekarar 2021, sakamakon gajeriyar rashin lafiya a Asibitin kasa da ke Abuja.[1][2][3][4]

Sa'idu Namaska
Rayuwa
Haihuwa 1 Disamba 1937
ƙasa Najeriya
Mutuwa 9 Satumba 2021
Sana'a

Tarihinsa gyara sashe

Saidu Namaska ya fara karatunsa ne a makarantar bida Middle School inda ya samu digirin BSc a jami'ar Ahmadu Bello dake a Zariya. Ya fara aiki a matsayin jami’in ‘yan sandan Najeriya a shekarar 1961, kuma ya zama shugaban shari’a na jihar Arewa maso Yamma kafin ya yi ritaya.

A cikin Janairun 1974, an naɗa shi Sarkin Sudan (sarkin baƙar fata) na Masarautar Kontagora kuma a matsayin Sarkin Kontagora na shida.

Yayin ziyarar yakin neman zaɓen tsohon gwamnan jihar Neja, Dr Muazu Babangida Aliyu, Saidu Namaska ya koka da samun ruwan rijiyar kawai don buƙatun gidan fadar sa da yake amfani da shi tsawon shekaru 36 da suka gabata a fadar.

Manazarta gyara sashe

  1. Newswatch (in Turanci). Newswatch Communications Limited. 1993.
  2. Obatomi, Femi (1993). The general at Works & Housing: Major-General M.T. Kontagora (rtd) (in Turanci). Foundation. ISBN 978-978-32005-0-0.
  3. Sani, Shehu (2007). The killing fields (in Turanci). Spectrum Books. ISBN 978-978-029-723-7.
  4. "Emir of Kontagora is dead". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2021-09-11.