Masarautar Kontagora
Masarautar Kontagora jiha ce ta gargajiya wacce ke dauke babban birnin Kontagora, Jihar Neja, a Nijeriya.[1][2] Masarautar Kontagora tana cikin manyan masarautun jihar Neja kamar Masarautar Kagara, Masarautar Suleja da sauransu.
Masarautar Kontagora | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jihohin Najeriya | Jihar Neja |
Tarihi
gyara sasheKontagora yanki ne wanda asalinsa ya rabu tsakanin ƙananan masarautu daban-daban (Aguarra, Dakka-Karri, Kambari, Dukawa, da Ngaski) wanda mutanen Fula suka ci su da yaƙi a tsakanishekarar n 1858 zuwa 1864, suka koma masarautar Kontagora, abin dogaro ga Daular Sokoto.[3][4]
Bayan wani hari da makami, tun daga ranar 31 ga watan Janairun shekarar 1901, Masarautar ta faɗa ƙarƙashin mulkin Birtaniya, inda kuma ta zama lardi na farko a cikin yankin Arewacin Najeriya na Birtaniyya sannan kuma a ƙarƙashin Turawan mulkin mallaka na Najeriya, har zuwa lokacin samun ‘yancin kan kai a shekarar 1960 da ƙasar ta samu.[5][6][7]
A yanzu dai Kontagora ta ƙunshi masarautun Kontagora mai ɗauke da masarautun Wushishi, da yankunan Sarkin Bauchi, da masarautar Kagara, duk a ƙarƙashin mulkinsu sun haɗe zuwa kananan hukumomin Mariga, Magama, da Rafi.[8]
Jerin sarakunan
gyara sasheSunayen sarakuna da lokutan zamanin mulkinsu da aka naƙalto daga; John Stewart's African States and Rulers (1989).[9]
No. | Suna | Fara mulki | Ƙarshen sarauta |
---|---|---|---|
1 | Umaru Nagwamatse | 1864 | 1876 |
2 | Abubakar Modibbo | 1876 | 1880 |
3 | Ibrahim Nagwamatse | 1880 | 1901 |
– | ba a gane ba | 1901 | Afrilu 1903 |
3 | Ibrahim Nagwamatse | Afrilu 1903 | 26 Oktoba 1929 |
4 | Umaru Maidubu | 26 Oktoba 1929 | Fabrairu 1961 |
5 | Mu'azu | Fabrairu 1961 | 1976 |
6 | Al-Hajji Saidu Namaska | 1976 | 7 Satumba 2021[10] |
7 | Muhammad Bara'u Mu'azu II | Oktoba 7, 2021[11] | har zuwa yau |
Manazarta
gyara sashe- ↑ SALAMONE, FRANK A. (1976), "Religious Change in a Northern Nigerian Emirate", The Realm of the Extra-Human, DE GRUYTER MOUTON, doi:10.1515/9783110805840.123, ISBN 978-3-11-080584-0
- ↑ "King-Lists, Chronicles and Other Minor Historical Works: Kontagora". Arabic Literature of Africa Online. doi:10.1163/2405-4453_alao_com_ala_20014_26.
- ↑ Brizvela-Garcia, Esperanza (2005-04-07), "Sokoto Caliphate", African American Studies Center, Oxford University Press, doi:10.1093/acref/9780195301731.013.43439, ISBN 978-0-19-530173-1
- ↑ Last, Murray. (1977). The Sokoto caliphate. Longman. OCLC 473688413.
- ↑ Brizvela-Garcia, Esperanza (2005-04-07), "Sokoto Caliphate", African American Studies Center, Oxford University Press, doi:10.1093/acref/9780195301731.013.43439, ISBN 978-0-19-530173-1
- ↑ Falola, Toyin; Tibenderana, P. K. (1991). "Sokoto Province under British Rule 1903-1939". The International Journal of African Historical Studies. 24 (1): 183. doi:10.2307/220113. ISSN 0361-7882. JSTOR 220113.
- ↑ July, Robert William (1998). A history of the African people. ISBN 0-88133-980-6. OCLC 43811431.
- ↑ Northern Nigerian Survey. (1966), Kontagora, Northern Nigerian Survey, OCLC 5568935
- ↑ Stewart, John (1989). African States and Rulers. London: McFarland. p. 154. ISBN 0-89950-390-X.
- ↑ "emir-kontagora-alhaji-namaska-dead". prnigeria.com. 7 September 2021. Retrieved 30 October 2021.
- ↑ Ahmadu Maishanu, Abubakar (7 October 2021). "Niger State Government announced Muhammad Barau as the seventh Emir of Kontagora". premiumtimesng.com. Retrieved 30 October 2021.