Remi Sonaiya
Oluremi Comfort Sonaiya (an haife shi a 2 ga Maris din shekarar 1955), yar siyasan Nijeriya ce, masaniyar ilmi kuma marubuciya.[1] Ta kasance mace ta farko da ta fara tsaya wa takarar kujerar shugaban kasa a Najeriya a zaben shekara ta 2015 a karkashin jam'iyyar KOWA.[2][3] Amma kwanan nan ta rasa takarar ta a hannun Dr. Adesina Fagbenro Byron don sake wakiltar jam’iyyar a zaben shekara ta 2019.[4][5]
Remi Sonaiya | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Ibadan, 2 ga Maris, 1955 (69 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Cornell Jami'ar Obafemi Awolowo |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa, marubuci da educational theorist (en) |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Sonaiya a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, inda ta kammala karatun ta na firamare da sakandire a makarantar St. Luke's Demonstration School, Ibadan da kuma St. A shekarar 1977, ta kammala karatun ta a Jami’ar Ife ( wacce a yanzu ake kira Jami’ar Obafemi Awolowo), inda ta karanci Faransanci.[6]
Daga baya ta samu digiri na biyu a fannin adabin Faransanci a jami’ar Cornell da ke Amurka, sannan ta sake samun digiri na biyu a fannin ilimin harsuna daga wata jami’a a Najeriya a shekarar 1984. Ta koma jami'ar Cornell ne a shekara ta 1988 don karatun PhD a fannin ilimin harshe.[7]
Ayyuka
gyara sasheA shekarar 1982, an dauke ta aiki matsayin mataimakiyar malami a Sashen Harsunan kasashen Waje, a Jami’ar Obafemi Awolowo kafin ta kai matsayin Farfesa a Fannin Harshen Faransanci da Kimiyyar Harshe a shekara ta 2004.[8] Ita mabiyar aikin Gidauniyar Alexander von Humboldt ce inda aka nada ta matsayin wakiliyar kimiya na gidauniyar na kimiyya daga shekara ta 2008 zuwa 2014.[7]
A shekara ta 2010 ne, ta yi ritaya daga matsayinta a Jami’ar Obafemi Awolowo kuma ta zama 'yar siyasa, a Jam’iyyar KOWA inda aka zabe ta a matsayin Jami’ar Hulda da Jama’a ta Kasa, sannan ta ci gaba da zama 'yar takarar Shugaban kasa a karkashin jam'iyyar a zaben shekara ta 2015.[9][10][11] A zaben, Sonaiya ta samu kuri'u 13,076 kuma ta kare a matsayi na 12.[12]
Littattafai
gyara sasheSonaiya marubuciya ce ga jaridar The Niche,[13][14] jaridar gidan yanar gizo ta Najeriya, Sonaiya ta buga littattafai da dama da suka hada da:
- Culture and Identity on Stage: Social-political Concerns and Enactments in Contemporary African Performing Arts (2001) ISBN 9789782015785
- Language Matters: Exploring the Dimensions of Multilingualism (2007)[15]
- A Trust to Earn – Reflections on Life and Leadership in Nigeria (2010)[16] ISBN 9789789115983
- Igniting Consciousness – Nigeria and Other Riddles (2013) ISBN 9785108473
- Daybreak Nigeria – This Nation Must Rise! (2014) ISBN 9789785205732
Rayuwa
gyara sasheTa auri Babafunso Sonaiya, farfesa a fannin kimiyyar dabbobi, kuma suna da ɗa daya, da mace ɗaya da jikoki.[6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Nigeria's first female presidential candidate done with 'cheerleading'". Vanguard News. March 18, 2015. Retrieved July 17, 2016.
- ↑ "McBain, Will (March 26, 2015). "Nigeria election: The country's first-ever female presidential candidate hoping to inspire other women to become politically active". The Independent. Retrieved July 17,2016.
- ↑ "Exclusive Interview With Professor Remi Sonaiya, KOWA Candidate For President of Nigeria". Sahara Reporters. February 7, 2015. Retrieved July 17,2016.
- ↑ "Fagbenro Byron Emerges as (KOWA) partys President candidate". Pulse.ng. Retrieved February 11, 2020.
- ↑ "Sanni, Kunle (September 30, 2018). "2019: KOWA Party announces presidential candidate". The Premium Times, Nigeria. Retrieved March 11, 2019.
- ↑ 6.0 6.1 "Biography". Retrieved July 17, 2016
- ↑ 7.0 7.1 "Varghese, Johnlee (March 12, 2015). "Nigeria Elections 2015: Who is Comfort Remi Sonaiya, the Only Female Presidential Candidate?". International Business Times. Retrieved July 17, 2016.
- ↑ "Agbonkhese, Josephine (February 8, 2015). "I'm rebuilding Nigeria into a nation that works— Remi Sonaiya, presidential candidate". Vanguard News. Retrieved July 17, 2016.
- ↑ "Ordinary Citiziens [sic] Like Me Can Be President Too – Sonaiya". Channels TV. January 7, 2015. Retrieved July 17, 2016.
- ↑ "Soyinka receives Presidential Candidate, Remi Sonaiya, in Lagos". Premium Times. March 26, 2015. Retrieved July 17, 2016.
- ↑ "Odunsi, Wale (May 25, 2016). "2019: Ignore APC, PDP, explore other options – Ex-presidential candidate, Remi Sonaiya urges Nigerians". Daily Post. Retrieved July 17, 2016.
- ↑ "Summary of Results" (PDF). Independent National Electoral Commission. p. 1. Retrieved July 18,2016.
- ↑ "Johnson-Salami, Laila. "Professor Remi Sonaiya, breaking down barriers for Nigerian women". rizing.org. Retrieved July 19, 2016.
- ↑ "There was no way I could have worked with Jonathan – KOWA Party's Remi Sonaiya – Olisa.tv". olisa.tv. Retrieved July 19, 2016.
- ↑ Remi Sonaiya (2007). Language Matters: Exploring the Dimensions of Multilingualism. Obafemi Awolowo University Press.
- ↑ "There was no way I could have worked with Jonathan – KOWA Party's Remi Sonaiya – Olisa.tv". olisa.tv. Retrieved July 19, 2016.