Ranar Sojojin Najeriya
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Ranar sojojin Najeriya biki ne da kuma taron shekara-shekara da aka saba gudanarwa a ranar 6 ga watan Yuli don karrama sojojin Najeriya musamman waɗanda suka yi yakin duniya na daya da yakin duniya na biyu gami da waɗanda suka rasa rayukansu a lokacin yakin basasar Najeriya, da kuma jami'an Sojojin Najeriya dake aiki a halin yanzu.[1][2]
Iri | maimaita aukuwa |
---|---|
Validity (en) | 1976 – |
Kwanan watan | 1976 – |
Tarihi
gyara sasheTarihin ranar sojojin Najeriya ya samo asali ne tun a shekarar 1863 lokacin da marigayi tsohon sojan Birtaniya John Hawley Glover ya kafa kungiyar" Glover Hausas " wanda ya shirya tare da tattaro 'yantattun bayin Hausawa don kare Kamfanin Royal Niger Company daga hare-haren mutanen Ashantis.[3] Tawagar wannan matashin domin daƙile farmakin masu kutse ne ya sanya aka kafa Sojojin Najeriya.[4] Ranar 6 ga watan Yuli ne aka amince da bikin ranar sojojin Najeriya saboda an yi imanin cewa, Glover Hausas, waɗanda suka yi kama da sojojin Najeriya, an kafa su ne a ranar 6 ga watan Yuli.[5] Haka kuma za a iya gano tarihin wannan rana tun ranar 6 ga watan Yulin 1967, wato ranar da aka fara yakin basasar Nijeriya.[6]
Ranar Soja a kowace shekara
gyara sashe2013
gyara sasheA shekarar 2013, yayin bikin a jihar Ogun dake kudu maso yammacin Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya ƙi amincewa da buƙatar gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun na ya ajiye fure a cibiyar taron da ke Abeokuta, bisa dalilin cewa ba a sanya shi a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka yi shimfidar ado ga jaruman da suka mutu ba.[7][8]
2015
gyara sasheAn gudanar da bikin a shekara ta 2015 a Maiduguri, mahaifar Boko Haram domin kara kwarin gwiwar sojojin Najeriya, yaki da ta'addanci, an kuma sako 'yan Boko Haram 128 da ke ɗaure a gidan yari a wani ɓangare na bukukuwan.[9][10]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Maiduguri grounded as Generals storm city for Nigeria Army Day". The Premium Times. Retrieved 9 June 2015.
- ↑ "Maiduguri Closed for Army Day Celebration". Thisdaylive. Archived from the original on 7 July 2015. Retrieved 9 June 2015.
- ↑ "celebrating nigerian army at 152". Thisdaylive. Archived from the original on 5 July 2015. Retrieved 9 June 2015.
- ↑ Oyewole, Olusegun (19 February 2012). The History of Nigerian Army - The Missing Link. LuLu. p. 51. ISBN 978-1471604294. Retrieved 7 June 2015.
- ↑ "Nigerian Army @ 152". The Guardian News.
- ↑ "182 Boko Haram suspects freed on Nigerian Army Day". Turkish Weekly. Archived from the original on 2015-07-29.
- ↑ "Drama as Obasanjo declines to lay wreath". The Punch News. Archived from the original on 10 July 2015. Retrieved 9 June 2015.
- ↑ "Mild Drama At Armed Forces Remembrance Day As OBJ Refuses". Information Nigeria. Retrieved 9 June 2015.
- ↑ "breaking nigerian military releases 182 boko haram prisoners maiduguri".
- ↑ "PHOTONEWS: President Jonathan At The 2013 Nigerian Army Day". Sahara Reporter.