Yakin Duniya na II
WW2Montage.PNG
world war
MabiyiYakin Duniya na I Gyara
followed bySecondo dopoguerra italiano Gyara
start time1 Satumba 1939 Gyara
end time2 Satumba 1945 Gyara
participantAxis, Allies Gyara
has causeTreaty of Versailles, causes of World War II, Hitler Gyara
has effectBritish Pet Massacre Gyara
Regensburg ClassificationNQ 2545 - NQ 2795 Gyara
tarihin maudu'itimeline of World War II, diplomatic history of World War II Gyara
described at URLhttps://stadtlexikon.karlsruhe.de/index.php/De:Lexikon:ereig-0074 Gyara
Stack Exchange taghttps://history.stackexchange.com/tags/world-war-two Gyara
category for mapsCategory:Maps of World War II Gyara
maintained by WikiProjectWikiProject World War II Gyara
WWII.jpg

Yakin Duniya na 2 da turanci World War II akan kintse rubutun kamar haka WWII ko WW2, har wayau anakiranta da turanci da Second World War. Yakin duniya dai wani yakine da duniya baki daya suka afka aciki wanda yakwashi tsawon shekaru shida (6) ana gwabzawa, tun daga shekara ta 1939 har zuwa shekarar 1945. Mafiya yawan kasashen duniya tare da kasashe masu karfi sune suka jadanga a tsakanin su, inda suke yakan juna: Hakane ya haifar da gagarumin gumurzu tsakaninsu wanda akalla mutane sama da miliyan dari ne (100,000,000) suka tsunduma aciki daga kasashe sama da talatin (30). Mafiya yawan kasashen da suka shiga cikin yakin sun saka dukkan tattalin arzikin su, da Masana'antunsu da ilimomin su na kimiyya da fasaha dan ganin sun samu galaba a yakin. Yakin duniya na II shine yaki mafi hatsari a duniya wanda Dan'adam bai taba gani ba, inda aka samu rasa rayukan mutane daga miliyan 50 zuwa miliyan 85, Wanda yawan cinsu fararen kayane daga Kasar Soviet Union wato Rasha ayanzu da kuma Kasar Sin. An sami kashe-kashe, kisan gilla akan Yahudawa, tsarin jefa bama-bamai, mutuwa sanadiyar yunwa da cututtuka, da kuma amfani da makamin kare-dangi a yakin.

Ansoma yakin daga ranar 1 ga watan September 1939 zuwa 2 September 1945 tsawon shekaru (6 years da kwana daya 1 )

Kasashen kawance sunyi nasara, an kifar da sojin Nazi dake Jamus, Ansamu faduwar Daulolin yakin Japan dana Italiya, Anfara amfani da Makamin kare dangi wato Nuclear weapon, Ikon karfin hanyar jirgin sama da kasashe kedashi, An rusa kungiyar League of Nations, An kirkira Majalisar Dinkin Duniya wato United Nations, Fara kiyayya tsakanin Kasar [[Amurika[] da Rasha, fara yakin mummuke. Jagororin Kungiyar kawance na Kasa da kasa,

  • Komandoji da Shugabanni

Kawaye shugabanni,

  1. Soviet Union Joseph Stalin
  2. United States Franklin D. Roosevelt
  3. United Kingdom Winston Churchill
  4. Jamhoroyar Sin (1912–1949) Chiang Kai-shek

Wanda ake fada dasu

  1. Nazi Germany Adolf Hitler
  2. Empire of Japan Hirohito
  3. Kingdom of Italy Benito Mussolini

Abubuwan da akayi asaransu Ankashe Sojoji: Sama da miliyan 16,000,000 An kashe farin kaye: Sama da miliyan 45,000,000 Adadin rayukan da aka rasa: Sama da miliyan kowa ki 61,000,000 (1937–1945)

Kasar Japan datake son ta mamaye nahiyar Asiya da yankin Pacific, tafara yaki da Kasar Sin tun daga 1937 duk da cewar babu bangaren da yafito fili yake kaddamar da yaki akan junansu. Andai ce yakin ya soma ne a 1 ga watan September 1939, da mamaye kasar Poland da kasar Jamus yayi, da kuma kaddamar da yaki da Kasar Faransa, Ingila sukayi akan kasar Jamus a karshen shekara ta 1939 har zuwa farkon shekara ta 1941, sai da irin gumurzu da shiri da Jamus din taitayi ne, hakan yasa yasamu nasara da mallakan kusan dukka nahiyar Turai, kuma suka kulla kawance da kasar Italiya da Japan a karkashin yarjejeniyar Molotov–Ribbentrop Pact of August 1939, Jamus da kasar Soviet sun rarraba yankunan Turai na kasashe kamar Poland, Finland, Romania da jihohin dake Baltic. Bayan cigaban da yaki akan kasashe dake yankin Afirka ta arewa da Afirka ta gabas, da kuma faduwar kasar Faransa a tsakiyar shekara ta 1940, Yakin yacigaba tsakanin Kasashe da Daular Biritaniya. Yaki a Balkans, a 22 ga watan June 1941, Kasashen hadaka suka kai hari akan kasar Soviet Union, wannan ne yazama wani gagarumin yaki da kasashe basu taba gani ba, akan jagorancin kasar Jamus. A kuma watan December 1941, Japan ta kaddamar da wani hari a kasar Amurika da wasu yankunan turawa dake yankin tekun Pacific. Hakane yasa kasar ta Amurika ta kaddamar da yakin gaggawa akan kasar Japan, kuma tasamu mara mata baya daga kasar Biritaniya, amma sai sai kasashen dake kawance da Japan na turawa suma sun mara was Japan din bayan, hakane yasa Japan ta kwace yawancin yankunan turawa dake yankin tekun Pacific, wanda yawancin kasashen Asiya suke ganinsa a matsayin wani shiri ne daga kasashen turai na taimakon sojojin da aka kifar da kasashen su.

Yaki ya tsaya a shekara ta 1942 bayan Japan ta mikawuya, kuma Jamus da Italiya suma anyi galaba akamsu a arewacin Afirka da gabashinta, a kuma garin Stalingrad dake Soviet Union. Anci karfin Jamus a shekara ta 1943, da kuma mamaye Sicily da Italiya, da nasara kasashen kawance a yankin Pacific, a 1944, kasashen kawance suka kwace yankin Faransa daga hannun Janus kuma itama kasar Soviet Union ta dawo da yamkunanta da daga hannun Jamus da kawayenta. Sai sai a shekara 1944 zuwa 1945 kasar Japan sunsha kashi sosai a yankin Asiya, musamman tsakiyar kasar Sin da kasar Burma, kuma aka kwato duk yankuman dake hannun su.

A inda yaki a nahiyar turai yakare ne sanadiyar mamaye Jamus da kasashen kawance da kasar Soviet suka yi wanda yakaiga kama garin Berlin da kisan Adolf Hitler da mikawuyar da Jamus tayi a 8 May 1945. Bayan Potsdam Declaration daga kungiyar kawance a 26 July 1945 da kuma kin da kasar Japan tayi nata mikawuya, yasa kasar Amurika ta jefa mata Malamin kare dangi wato atomic bombs a garuruwan Hiroshima da Nagasaki a 6 da 9 ga watan Augusta. Da kuma mamaye archipelago imminent, da ganin irin asara da rayuka da aka rasa kuma da cigaba da mamaye war yankuna da kasar Soviet tacigaba dayi a garin Manchuria da tsibirin Kuril dake arewacin kasar ta Japan, Yasa Sarkin Kasar a 2 September 1945 yamika wuya, wannan yabada nasara kasashen kawance a nahiyar Asiya, kuma sai aka fara tuhumar kasar Japan da Jamus akan laifukan yaki.

ManazartaGyara

Wannan ƙasida guntu ne: yana buƙatar a inganta shi, kuna iya gyarashi.