Paul Pogba
Paul Labile Pogba (Faransanci: pɔl pɔgba); An haife shi a ranar 15 ga watan Maris shekarar 1993) ƙwararren ɗan'wasan ƙwallon ƙafan ƙasar Faransa ne wanda ke buga wasansa a kungiyar kulub ta ƙasar Ingila Manchester United da ƙasar sa Faransa. Yana buga wasan tsakiya ne acikin filin wasa, sannan kuma yana iya buga wasa a tsakiya kuma mai kai fara cin ƙwallo, da tsakiya mai tsaron gida, da kuma babban mai gudanar wa acikin fili.[1]
An haife shi a garin Lagny-sur-Marne, Pogba ya nuna hazaƙa sosai a yarin tarsa, inda ya taso daga kungiyan matasa masu ƙwazo. Pogba ya fara yin wasa a kungiyar Ligue 1 wato Le Havre a sanda yake yaro, kafin nan ya koma Manchester United a 2009. Bayan kwashe shekara biyu da fara buga wasansa a Manchester United, amma ƙarancin buga wasansa yasa ya koma Juventus a kyauta shekara ta 2012, anan ne yataimaka wa kulub ɗin samun nasarar lashe gasar Serie A har sau hudu, da kuma gasar Coppa Italia da gasar Supercoppa Italiana guda biyu. A sanda yake kasar Italiya, Pogba ya maida kansa amatsayin daya daga cikin ƙwararrun matasa masu ƙwazo a duniya, inda yasamu kyautar Golden Boy award a shekarar 2013, sannan kuma yasamu Bravo Award a 2014. A 2016, Pogba ya shiga cikin ƙwararrun yan'wasa na 2015 UEFA Team of the Year, da na 2015 FIFA FIFPro World XI, bayan taimakon Juventus zuwa 2015 UEFA Champions League Final, wanda shine zuwan su na farko a bayan shekaru 12. Ya jagoran ci kasar yasa faransa zuwa wasan duniya,
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Paul Pogba (Manchester United FC)". Guineefoot.info (in French). 30 January 2009. Retrieved 2 August 2010.CS1 maint: unrecognized language (link)