Olusegun Mimiko
Olusegun Mimiko ( Yoruba;) an haife shi ranar 3 ga watan Oktoba na shekarar 1954, shi ne dan takarar sanata na Zenith Labour Party a Ondo ta Tsakiya a zaben shekarar 2019.[1]Shi ɗan siyasan Nijeriya ne wanda ya yi aiki na 16, kuma na biyar a farar hula, Gwamnan Jihar Ondo, Nijeriya, daga watan Fabrairu shekarar 2009, zuwa Fabrairu shekarar 2017. Gwamna na farko a zango biyu na jihar Ondo kuma gwamna na farkon Jam’iyyar Labour a Najeriya. Mimiko ya taba zama ministan tarayya na gidaje da, sakataren gwamnatin jihar Ondo, sannan ya taba zama kwamishinan lafiya na jihar Ondo sau biyu. Ya ci gaba da sha'awar siyasa tun yana ƙaramin. dan siyasa ya fara ne a makarantar likitanci a Jami'ar Ife (yanzu Obafemi Awolowo University), inda ya kasance memba na Majalisar Wakilai ta (Majalisar) kuma ya yi aiki a matsayin jami'in hulda da jama'a na kungiyar International Students’ Association of the institution daga shekarar 1977 zuwa shekara ta 1978.
Olusegun Mimiko | |||
---|---|---|---|
ga Faburairu, 2009 - ga Faburairu, 2017 ← Olusegun Agagu (en) - Oluwarotimi Odunayo Akeredolu → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 3 Oktoba 1954 (70 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Yaren Yarbawa | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Obafemi Awolowo (1972 - 1976) | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Addini | Kiristanci | ||
Jam'iyar siyasa | Nigeria Labour Party |
Bayan kammala karatunsa a jami'a a shekarar 1980 kuma ya kammala National Youth Service Corp, Mimiko ya fara aikin likita. A cikin 1985, ya kafa MONA MEDICLINIC a cikin garin Ondo wanda yayi aiki a matsayin cibiyar taimakon al'umma. [2]
Nadin Mimiko na siyasa na farko shi ne kwamishina na kiwon lafiya da walwala da jin dadin jama'a a jihar Ondo daga shekarar 1992 zuwa shekara ta 1993 lokacin da wani juyin mulkin soja ya kawo karshen mulkin dimokiradiyya ta Uku . Bayan dawowar mulkin dimokiradiyya a Najeriya, Mimiko ya sake zama kwamishinan lafiya a jihar Ondo daga shekarar 1999 zuwa shekara ta 2002.
A shekarar 2003, aka nada shi sakataren Gwamnatin Jihar Ondo (SSG). Ya rike wannan mukamin har zuwa watan Yulin shekarar 2005, lokacin da aka nada shi a matsayin ministan gidaje da ci gaban birane na tarayya. [2] Mimiko ya yi murabus daga mukaminsa na ministan tarayya don ya yi takarar gwamnan Ondo da mai ci, Olusegun Agagu a zaben shekarar 2007 .[3]
Mimiko ya lashe zaben. Amma, tasirin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta sanar da Agagu a matsayin wanda ya yi nasara. Mimiko ya kalubalanci sakamakon zaben a kotuna kan abin da ya kasance rikicin shekaru biyu na shari’a wanda ya kawo karshen bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben na gwamna ta hanyar hukuncin daya yanke na Kotun, da kuma Kotun daukaka kara a shekarar 2009.[4] [5]Ya ci gaba da sake lashe zaben a shekarar 2012, inda ya doke babban abokin karawarsa, Olusola Oke na Jam’iyyar Democratic Party.
A lokacin mulkin Mimiko a matsayin gwamna, sauye-sauyen da ya yi a bangaren kiwon lafiya, ilimi, ci gaban al'umma, sabunta birane da kuma amfani da fasaha a harkokin mulki sun samu karbuwa a kasashe na duniya.[6][7][8][9][10][11][12]
Bayan ya bar ofis, Mimiko ya kwashe shekara guda yana gabatar da laccocin jama'a tare da yin kira kan kiwon lafiyar duniya da kyakkyawan shugabanci a Najeriya, London, da Washington DC.[13][14]
A watan Satumba na shekarar 2018, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2019.[15]Ya amshi takara a matsayin dan takarar shugaban kasa na Labour Zenith Party a watan Oktoba, shekarar 2018.[16]A ranar 14 ga watan Nuwamba, shekarar 2018, Mimiko ya sanar da cewa ya dakatar da yakin neman zabensa na shugaban kasa, 'yan kwanaki kafin a bude kakar yakin neman zabe a hukumance. Ya dauki tikitin takarar sanata na Zenith Labour Party na mazabar tarayya ta Ondo ta Tsakiya.[17] Mimiko a halin yanzu yana zaune a Ondo City,a mahaifar sa.
Rayuwar mutum
gyara sasheAn haifi Rahman Olusegun Mimiko, wanda aka fi sani da Iroko, a ranar 3 ga watan Oktoba, na shekarar 1954, a garin Ondo da ke Jihar Ondo, Najeriya . Mahaifinsa, Atiku Bamidele Mimiko, ɗa ne ga Pa Famimikomi, ɗa ne ga Cif Ruwase Akinmeji kuma jika ne ga Babban Cif Adaja Gbegbaje na Masarautar Ondo . [2] Mahaifin Mimiko ya kasance manajan dillalai kuma manomi ne na shuka koko. Ya kuma kasance mai sharhi kan zamantakewar al'umma da ci gaban kasa da kuma taimakon jama'a. Mahaifiyarsa, Muinat Mimiko (née Ogunsulie) 'yar kasuwa ce har zuwa lokacin da ta yi ritaya.[18]A shekarar 1990, Mimiko ya auri Olukemi Adeniyi wacce ta karanci harshen Faransanci a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile Ife . Suna da yara hudu.[19]
Ilimi
gyara sasheMimiko ya fara makaranta a St. Joseph's Primary School Aponmu kusa da Akure, St. Patrick Primary School, Yaba a Ondo a farkon shekarar 1960s. Ya halarci kwalejin St. Joseph's, Ondo daga shekarar 1966 da shekara ta 1971. Ya kasance dalibin makarantar sakandare (HSC) a makarantar Gboluji Grammar, Ile-Oluji tsakanin shekarar 1971 da shekara ta 1972. Mimiko ya fara karatun likitanci a Jami'ar Ife a shekarar 1972. Ya kasance wakilin Dalibai (majalisa) daga shekarar 1975 da shekara ta 1976 kuma shugaban kwamitin girmamawa na musamman (1976-1977), memba na Kwamitin Zabe na Kungiyar Daliban 1976-1977 kuma jami'in hulda da jama'a na kungiyar Dalibai ta Duniya a shekarar 1977 da shekara ta 1978. [2] Ya sami B.Sc. Digiri na Kimiyyar Kiwan Lafiya a shekarar 1976, da kuma Kimiyyar Likita, yayi aikin likita a shekarar 1980. Mimiko yayi rijista da kungiyar likitocin Najeriya da likitan hakori a matsayin likita.[20][21]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Mimiko Pulls out of Presidential Race for Senate". ThisDay (in Turanci). Retrieved 2018-11-29.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 Olu, Obafemi. Mimiko‘s Odyssey, A Biography of Revelations, 2017. Print.
- ↑ Olu, Obafemi. Mimiko‘s Odyssey, A Biography of Revelations, 2017. Print. Samfuri:Verify source
- ↑ Tenuche, M. "Language of Politics and Political Behaviours: Rhetoric of President Olusegun Obasanjo and the 2007 General Elections in Nigeria." Journal of public administration and policy research 1.3 (2009): 54-65.
- ↑ "President Obasanjo's Utterances on General Elections in April 2007: A Call to Order". Senate of the Federal Republic of Nigeria5TH NATIONAL ASSEMBLY FOURTH SESSION NO. 128 (in Turanci). Retrieved 2018-05-21.
- ↑ "FG Should Emulate Mimiko's Progressive Initiatives– UNICEF Country Rep". Vanguard (Nigeria) (in Turanci). Retrieved 2018-05-21.
- ↑ "Kaadi Igbe Ayo: Mimiko's Revolutionary Use Of Technology in Governance". The Trent (in Turanci). Retrieved 2017-09-18.
- ↑ "SPAGnVOLA shop in Gaithersburg finds a niche in chocolate making". The Washington Post (in Turanci). Retrieved 2018-07-21.
- ↑ "Developer transforms Ore to N20 billion Sunshine City". The Guardian (Nigeria) (in Turanci). Archived from the original on 2018-07-26. Retrieved 2018-04-21.
- ↑ Okereke, Dominic. Africa's Quiet Revolution Observed from Nigeri. Paragon Publishing, 2012.Pg.659
- ↑ "Mimiko inaugurates N5bn Ore mega plaza project". Vanguard (Nigeria) (in Turanci). Retrieved 2018-04-21.
- ↑ "Nigeria: Mimiko Takes Delivery of Turbine for Ore". AllAfrica.com (in Turanci). Retrieved 2018-04-21.
- ↑ Emmanuel, Afe Adedayo. "GOVERNORSHIP ELECTION LITIGATION AND POLITICAL STABILITY IN ONDO STATE NIGERIA, 1983-2013." International Journal of Arts & Sciences 8.2 (2015): 139.
- ↑ "Mimiko and the market of old wisdom". The Guardian (Nigeria) (in Turanci). Archived from the original on 2018-07-26. Retrieved 2018-04-21.
- ↑ "Olusegun Mimiko Declares For President, Reiterates Commitment To Social Democratic Ideals". thetrentonline.com. Retrieved 2018-09-13.
- ↑ "BREAKING: Mimiko Emerges As The Presidential Candidate Of Zenith Labour Party". thetrentonline.com. Retrieved 2018-10-11.
- ↑ "Mimiko Pulls out of Presidential Race for Senate". ThisDay (in Turanci). Retrieved 2018-11-29.
- ↑ "Synopsis of Dr. Olusegun Rahman Mimiko (a.k.a. Iroko) - Ekimogun Descendant United Kingdom & Northern Ireland". ekimogundescendant.org.
- ↑ Olu, Obafemi. Mimiko‘s Odyssey, A Biography of Revelations, 2017. Print.
- ↑ "Synopsis of Dr. Olusegun Rahman Mimiko (a.k.a. Iroko) - Ekimogun Descendant United Kingdom & Northern Ireland". ekimogundescendant.org.
- ↑ "The Man "Iroko" Rahman Olusegun Mimiko". www.pointblanknews.com.