Nkoyo Esu Toyo (an haife tane a 5 ga watan Nuwamba 1958) yar siyasan Nijeriya ce, lauya ce kuma mai ba da shawara game da ci gaban al'amura, tare da keɓaɓɓu a kan haƙƙin ɗan adam da daidaiton jinsi [1]Ita tsohuwar jakadiyar Najeriya ce a Habasha, kuma ita ce ta kafa kungiyar Gender and Development Action (GADA) a Nijeriya[2]An zabe ta ne don wakiltar Municipality / Odukpani Federal Constituency of Cross River yayin zaɓen 2011[3] Nkoyo Toyo ƙwararriyar masaniyar mulki ce tare da kasancewa membobi a cikin ƙungiyoyin mata.[4] da yawa kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kira taron “Mata dubu goma” a Abuja, wanda ƙungiyar Women4Women (W4W) He4She ta shirya don magance matsalolin da suka shafi mata[5]

Nkoyo Toyo
Rayuwa
Haihuwa Jahar Cross River, 5 Nuwamba, 1958 (66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Sussex (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu Bello
Jami'ar jahar Lagos
Makarantar Koyan Lauya ta Najeriya
Matakin karatu Master of Laws (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Lauya, ɗan siyasa da gwagwarmaya

A 1974, Nkoyo ta kammala makarantar sakandare ta Union sannan ya ci gaba da karatun lauya a jami'ar Ahmadu Bello, Zariya Kaduna a shekarar 1975. A shekarar 1980, Nkoyo Toyo ta kammala karatun ta a makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya kuma aka kira ta zuwa kungiyar lauyoyin Najeriya . Daga baya ta sami digiri na biyu na (Law of Laws (LLM) a Jami'ar Legas a 1994[6] .Saboda sha'awarta da aikinta na ciyar da matsayin mata a rayuwar jama'a ta Najeriya, Nkoyo ta sami Chevening Scholarship don yin karatu a Cibiyar Nazarin Ci Gaban (IDS), Jami'ar Sussex[7].inda ta karɓi Masters a Gudanarwa a 2001 . Daga shekarar 2020 zuwa 2021, ta sami digirin digirgir a fannin tafiyar da harkokin gwamnati (MPA) daga makarantar John F. Kennedy ta gwamnati a jami’ar Harvard .

Manazarta

gyara sashe
  1. Oyewole, Nurudeen. "New laws are expensive – Nkoyo Toyo". Daily Trust. Archived from the original on 2 July 2018. Retrieved 8 March 2018.
  2. Igbinovia, Josephine (25 August 2013). "Nigeria has too many laws already – Hon. Nkoyo Toyo". Vanguard. Retrieved 13 May 2018.
  3. "Appeal courts upholds elections of Rep. Nkoyo Toyo". Sharpedgenews.com. Retrieved 13 May 2018.
  4. Cornwall, Andrea; Molyneux, Maxine (13 September 2013). The Politics of Rights: Dilemmas for Feminist Praxis. USA Canada: Routledge. p. ix. ISBN 9781317996750. Retrieved 13 May 2018.
  5. Onifade, Olasunkanmi (10 May 2018). "Women group demand progress, implementation of charter". SundiataPost. Archived from the original on 1 July 2019. Retrieved 13 May 2018.
  6. "Hon. Esu Toyo Nkoyo". Nigeria Governanace Project. Retrieved 8 March 2018.
  7. "Our Board". Civil Society Legislative Advocacy Centre. Archived from the original on 16 March 2018. Retrieved 8 March 2018.