Muhammad Bello Yabo
Muhammad Bello Aliyu Yabo wanda aka fi sani da Bello Yabo (an haife shi a ranar 1,ga watan Junairu shekara ta 1962). Malamin Addinin Musulunci ne a Najeriya kuma ana lissafo shi cikin manyan malaman Najeriya. Malam Bello Yabo ya kuma soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya, wato (Arewa maso Yammacin Najeriya) musamman a jihohin Zamfara, Sokoto, Kaduna, Katsina da Jihar Neja.[1]
Muhammad Bello Yabo | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a |
Ilimi da Aiki
gyara sasheBello Yabo ya yi makarantar Islamiyya tun yana ƙarami. Bayan ya kammala sai Malam Bello Yabo ya fara makarantar firamare a makarantar firamare ta garin Yabo daga bisani ya wuce makarantar Government Day Secondary School duka dai a garin na Yabo. An kuma naɗa Bello Yabo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan kula da hanyoyin karkara.[ana buƙatar hujja] Ya yi aiki a matsayin mai kula da kuɗi na cikin gida a ƙaramar hukumar Dange-Shuni, ya riƙe Daraktan kuɗi na musamman na asibitin Sokoto, daraktan kuɗi ma'aikatar ilimi ta Sokoto. Sheikh Bello yabo yana cikin sahun malamman da suka yi yaƙi da Akidar boko haram a Nigeria.
Sukar El-Rufa'i
gyara sasheA shekarar 2020 yayin da annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta ɓulla a jihar Sokoto, Bello Yabo, babban malamin addinin Islama na jihar Sokoto, bayan wani faifan bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya yana kiran sauran mabiya addinin Musulunci da su fito ƙwansu da ƙwar-ƙwarta su don Sallar Eid-el-Fitr bayan sun yi azumin watan Ramadan.[2] Wanda har ya nuna cewa cutar bata yaɗu ba a Najeriya saboda haka babu dalilin da za'a hana mutane yin Addinin su. Haka kuma a wani wani faifan bidiyo wanda kuma ya yi Allah wadai da hana Sallar Idi, a Jihar Kaduna. Wanda a faifan bidiyon ya caccaki Gwamnan jihar Kaduna El-Rufae da sauran gwamnoni kan hana Sallar Idi a jihohinsu. Rundunar ƴan sandan Najeriya ta gayyaci Bello Yabo saboda wannan faifan bidiyon na rana ɗaya wanda ya sifanta gwamnan Kaduna El-Rufa'i da "ɗan ƙaramin tsuntsu".[3][4][5][6][7]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ Ammani, Ibrahim (9 December 2021). "Buhari Ya Ci Amanar 'Yan Najeriya – Sheikh Bello Yabo". Muryarƴanci.com. Retrieved 23 May 2022.
- ↑ "Islamic Cleric, Sheik Bello Yabo, Arrested For Condemning Eid Prayers Ban". saharareporters.com. 22 May 2020. Retrieved 23 May 2022.
- ↑ Bello, Nasiru (25 May 2020). "Makirci Aka Shirya Da Aka Kama Ni —Malam Bello Yabo". Aminiya.dailytrust.com. Retrieved 23 May 2022.
- ↑ Usman, Jamil (23 May 2020). "An damke malamin da ya yi wa El-Rufai 'wankin babban bargo' a kan hana sallar Idi". legit.hausa.ng. Retrieved 23 May 2022.
- ↑ Hassan, Maryam (23 May 2020). "Sokoto-based Islamic scholar, Bello Yabo, arrested for criticizing El-Rufai" (in Turanci). dailynigerian.com. Archived from the original on 23 May 2022. Retrieved 23 May 2022.
- ↑ Ikeke, Nkem (23 May 2020). "Islamic cleric arrested in Sokoto for criticising Governor El-Rufai". legit.ng. Archived from the original on 23 May 2022. Retrieved 23 May 2022.
- ↑ Holland, Kitty (26 May 2020). "Islamic scholar arrested for criticising El-Rufai regains freedom". thestreetjournal.org. Retrieved 23 May 2022.