Muhammad Ayyub bn Muhammad Yusuf bn Sulaiman `Umar ( Larabci: محمد أيوب بن محمد يوسف بن سليمان عمر‎ ) Limamin ƙasar Saudiyya ne, Mahaddaci, kuma malamin addinin musulunci wanda ya shahara wajen karatun Alqur'ani . Ya kasance limamin Al-Masjid an-Nabawi (Masallacin Manzon Allah S A W) Madina, Saudi Arabia. Ya kuma kasance malami a sashin Tafsiri a tsangayar Qur'ani mai tsarki da ilimin addinin musulunci na Jami'ar Musulunci ta Madina sannan kuma mamba ne a kwamitin malamai na cibiyar buga Alqur'ani mai girma ta sarki Fahd. Ya rasu a ranar 16 ga watan Afrilu, shekarar, 2016.

Muhammad Ayyub
Rayuwa
Haihuwa Makkah, 1 ga Janairu, 1952
ƙasa Saudi Arebiya
Harshen uwa Larabci
Mutuwa Madinah, 16 ga Afirilu, 2016
Makwanci Al-Baqi'
Karatu
Makaranta Jami'ar Musulunci ta Madinah
Harsuna Larabci
Malamai Khalil Al-Qari
Sana'a
Sana'a Liman da Liman
Imani
Addini Musulunci
wurin aje Mayan tarihin.musulunci
garinsu mohammadu

Tarihin Rayuwarsa

gyara sashe

An haifi Muhammad Ayyub a shekara ta, 1952 ko, 1953 (1372 bayan hijira ) a birnin Makkah na kasar Saudiyya. Ya rasu a ranar 16 ga Afrilu, shekarar, 2016 a birnin Madina na ƙasar Saudiyya.[1]

Mahaifinsa talaka ne wanda iyalansa suka yi hijira daga kasarsu ta haihuwa "Arakan" da ke a Burma zuwa Makka don gudun zalunci da ake yi wa Musulman Rohingya na Burma. Ya sha wahalar rayuwa a lokacin ƙurciyar shi tare da yayanninsa da suke aiki tuƙuru don taimakawa gidansu, lokacin da aka tsare mahaifinsa a kurkuku a Burma.

Ya kammala haddar Alqur'ani a shekara ta 1385 bayan hijira (1965 zuwa 1966) a ƙarƙashin Khalil ibn 'Abd ar-Rahman al-Qari' a Makka. Bayan kammala karatunsa na firamare a shekarar, 1386 bayan hijira (1966 zuwa 1967) ya koma Madina, inda ya kammala karatunsa na sakandare a makarantar Islamiyya, inda ya kammala a shekara ta, 1392 bayan hijira (1972).

Sannan ya karanta ɓangaren Shari'a a Jami'ar Musulunci ta Madina, inda ya sami digiri na farko a shekarar, 1396 bayan hijira (1976). Sannan ya samu ƙwarewa a fannin Tafsiri da 'Ulum al-Qur'an (tafsirin Alqur'ani da ilimomin Alqur'ani), inda ya samu digiri na biyu a Sashen Qur'ani da Ilimin addinin Musulunci. Ya sami digiri na uku a tsayayya da ta yayi digiri a shekarar, 1408 AH (1987 zuwa 1988).

Bayan karatunsa a makaranta, ya kuma yi karatun zaure a gaban wasu malaman Musulunci da dama a Madina, a fannonin da suka haɗa da tafsiri da ilimomin da ke da alaka da su, fiqhun mazhabobi huɗu, tafsirin hadisi, da usulul fiqhu.

A shekara ta, 1410 bayan hijira (1990) an naɗa shi limamin Al-Masjid an-Nabawi. Ya riƙe wannan mukami har zuwa shekara ta, 1417 bayan hijira (1997). Sannan ya yi shekaru kaɗan yana Limami a Masallacin Quba da sauran masallatai. An nada shi a matsayin limamin Al-Masjid an-Nabawi a shekara ta, 2015 (1436 hijiriyya) don jagorantar sallar tarawihi.

Muhammad Ayyub dan ƙasar Burma ne kuma mabiyin mazhabar Imam Hanbali.

Ya rasu a ranar 16 ga watan Afrilu shekarar, 2016 kuma an binne shi a makabartar Baqi da ke Madina.

Manazarta

gyara sashe
  1. Harun Abu Ayyub (8 April 2010). "نبذة عن فضيلة الشيخ". mdayyoub.com. Archived from the original on 5 July 2012. Retrieved 16 August 2012.