Mohammed Abul-Salam Onuka
Mohammed Abul-Salam Onuka sojan Najeriya ne wanda ya yi aiki a matsayin shugaban mulkin soja na jihar Edo tsakanin watan Disambar 1993 zuwa watan Satumban 1994. Ya karɓi mulki daga hannun gwamnan farar hula, John Odigie Oyegun, a farkon mulkin soja na Janar Sani Abacha.[1]
Mohammed Abul-Salam Onuka | |||
---|---|---|---|
9 Disamba 1993 - 14 Satumba 1994 ← John Odigie Oyegun - Bassey Asuquo → | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Mohammed Abul-Salam Onuka | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Hausawa | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Kanal Onuka ya yi ƙoƙari na haɓaka damar yawon buɗe ido na yankin Ososo, to amma ƙoƙarin bai daɗe ba saboda ba zato ba tsammani da gwamnatin Abacha ta yi.[2] Daga Okene a jihar Kogi kuma kani na farko zuwa gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello (APC).