Muhammad Bara'u Mu'azu

Sarkin Sudan

Alhaji Muhammad Barau Mu'azu II Sarkin Sudan na bakwai (Sarkin Kontagora) an haifeshi a shekarar 1974 a garin Kwantagora dake jihar Neja ga Iyalan marigayi Mu'azu Ibrahim. Jikan marigayi Sarkin Sudan Ibrahim Nagwamatse wanda ya shugabanci Masarautar ta Kontagora.[1][2]

Muhammad Bara'u Mu'azu
Rayuwa
Haihuwa 1974 (49/50 shekaru)
Sana'a

Karatu gyara sashe

Muhammad Bara'u Mu'azu II ya samu takardun shedar karatuttuka da dama a matakai daban-daban. Muhammadu Barau Mu'azu ya yi karatun firamare daga shekarar 1980 zuwa 1986 a makarantar firamare da ke garin Ibeto. Daga nan sai ya shiga makarantar sakandare a makarantar gwamnati ta Kontagora, inda ya yi karatu daga shekarar 1986 zuwa 1992. Daga 1994 zuwa 1997, Ya wuce Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Kontagora, inda ya samu takardar shaidar kammala karatun NCE.[3][4]

Aiki gyara sashe

Ya yi aiki da Kamfanin Salwa Global, inda ya riƙe muƙamin Janar Manaja.

Mulki gyara sashe

Bayan rasuwar Sa'idu Namaska ba tsohon sarkin Sudan na Kontagora a shekarar 2021, kusan mutane 43 ne suka miƙa takardun neman kujerar sarautar Kontagora.[5] Gwamnatin Abubakar Sani Bello ta amince da Muhammadu Barau Muazu II a matsayin magajin Marigayin, bayan da majalisar masu zaɓar sarki ta zaɓe shi.[6] Kakansa, Mu'azu Ibrahim shi ne Sarkin Kontagora na 5, wanda ya shafe kimanin shekaru 13 a kan karagar mulki daga shekarar 1961 zuwa 1974. Sai dai sauran ƴan takarar ba su amince da zaɓen kujerar sarauta ba, don haka suka yanke shawarar kai kokensu a gaban kotu.[7] Bayan kotu ta dakatar da naɗin nasa, shari’ar da kotun ta yi ta tabbatar da nadin nasa a matsayin sarkin Kontagora na bakwai.[8]

Manazarta gyara sashe

  1. "Mohammed Barau Is The New Emir Of Kontagora". dailytrust.com. 6 October 2021. Retrieved 7 October 2023.
  2. "@Sarkin Sudan's installation: Governor charges monarchs to steer clear of politics". blueprint.ng. 12 February 2023. Retrieved 7 October 2023.
  3. Mohammed Isah, Abdul (12 February 2023). "Emir Of Kontagora In Niger State Gets Staff Of Office". Voice of Nigeria. Retrieved 7 October 2023.
  4. Mulumfashi, Muhammad (14 February 2023). "Sabon Sarki ya Gaji Karagar Kakansa Bayan Jiran Kusan Shekaru 50 a Kontagora". hausa.legit.ng. Retrieved 7 October 2023.
  5. Asishana, Justina (19 September 2021). "Full list of contestants for Emir of Kontagora". the nation online nv. Retrieved 7 October 2023.
  6. Ahmadu Mai-shanu, Abubakar (7 October 2021). "Nigeria: Niger Government Announces New Emir of Kontagora". allafrica.com. Retrieved 7 October 2023.
  7. Ahmadu Mai-shanu, Abubakar (13 October 2021). "Court halts appointment of new Emir of Kontagora". premiumstimesng.com. Retrieved 7 October 2023.
  8. Rashid, Abdurrahman (20 October 2021). "Kotu ta mayar da Mohammed Barau matsayin SarkinSudan na Kontagora". hausa.legit.ng. Retrieved 7 October 2023.