Majalisar Koli ta Soja ta Najeriya (1966-1979)

Mataimakin shugaban soja a Najeriya (1966-1979)

Majalisar koli ta soja ita ce hukumar da ta mulki Najeriya bayan juyin mulkin shekarar 1966 har zuwa lokacin da aka rusa ta bayan zaɓen 1979 na 'yan majalisar dokoki da jamhuriya ta biyu ta Najeriya. Majalisar ƙoli ta soja ta kasance a Barikin Dodan a matsayin hedikwatar koli na soja (SMHQ) a Legas.

Majalisar Koli ta Soja ta Najeriya (1966-1979)
Bayanai
Farawa 1966

Bisa ga dokar tsarin mulki, wanda aka buga a Legas a ranar 17 ga Maris 1967, ikon majalisa da zartarwa ya kasance ga Majalisar Koli ta Sojoji. Shugaban majalisar ya kasance shugaban gwamnatin soja.

Majalisar ƙoli ta soja ta ƙunshi hakiman soji na yankin da shugaban mulkin soji na tarayyar Najeriya, da shugabannin sojojin Najeriya da na ruwa da na sama da babban hafsan soji da sufeto-janar na ‘yan sanda ko mataimakinsa.

Majalisar Koli ta Sojoji na iya ba da iko ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya, wadda galibi ta ƙunshi kwamishinonin farar hula.

Shugaban majalisar ƙoli ta soja na farko shi ne Maj.-Gen. Yakubu Gowon, Babban Kwamandan Sojojin Najeriya. An maye gurbinsa da Murtala Muhammed (a shekarar 1975 ) da Olusegun Obasanjo (a 1976 ) a juyin mulki a jere.

Bayan juyin mulkin 1983 Muhammadu Buhari ya kafa wata majalisar koli ta soja wacce ta daɗe har zuwa juyin mulkin 1985.

Suna Mukami
Yakubu Gowon Shugaban Gwamnatin Tarayya (1966-1975)
Murtala Mohammed Head of State (1975–76)
Rear-Admiral Joseph Edet Akinwale Wey Babban Hafsan Sojan Ruwa (1964 – 1973), Shugaban Ma’aikatan Hedikwatar Koli (1973–75)
Nelson Bossman Soroh Babban Hafsan Sojan Ruwa (1973-1975)
Michael Ayinde Adelanwa shugaban sojojin ruwa (1975-1980)
Brig. Hassan U. Katsina Gwamnan Sojan]], Arewa (1966-67), Shugaban Hafsan Soja (1968-71)
Brig. Emmanuel Ekpo shugaban ma'aikata na hedikwatar koli
Joseph Akahan Chief of Army Staff (1967–68)
Col. Illiya Bisalla Kwamishinan Tsaro (1975-76)
Olusegun Obasanjo Shugaban Ma'aikata, Babban Hedikwata (1975-1976), Shugaban Kasa (1976-79)
Theophilus Danjuma Chief of Army Staff (1975–79)
Ipoola Alani Akinrinade babban hafsan soji (1979-1980)
George T. Kurubo Shugaban Rundunar Sojan Sama (1966-67)
Col. Shittu Alao Shugaban hafsan sojin sama (1967–69)
Emmanuel E Ikwue Shugaban Hafsan Sojan Sama (1969-1975)
John Nmadu Yisa-Doko Shugaban Hafsan Sojan Sama (1975-1980)
Alhaji Kam Salem Sufeto-Janar na 'yan sanda (1966-1975)
Muhammadu Dikko Yusufu Sufeto-Janar na 'Yan Sanda (1975-1979)
David Ejoor Gwamnan Soja na Yankin Yamma ta Tsakiya, Najeriya (1966-1971), Babban Hafsan Soja (1971-1975)
C. Odumegwu Ojukwu Gwamnan Soja na yankin Gabashin Nijeriya
Adekunle Fajuyi Gwamnan Soja na Yankin Yamma

Gwamnonin soji na jihohi goma sha biyuu, na tarayya sun kasance tsofaffin mambobin kwamitin.

  • The Europa World Year Book 1970