Shittu Alao

Tsohon hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya

Shittu Alao (an haife shi a shekara ta 1937 – 15 ga Oktoba 1969) shi ne babban hafsan hafsoshin sojin saman Najeriya daga shekara ta 1967 zuwa 1969.[1] Kanar Shittu shi ne kwamandan rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) na huɗu, kuma jami’i na biyu ɗan asalin ƙasar da ya riƙe wannan muƙamin.

Shittu Alao
Chief of the Air Staff (en) Fassara

5 ga Augusta, 1967 - 15 Oktoba 1969
Rayuwa
Haihuwa 1937
ƙasa Najeriya
Mutuwa 15 Oktoba 1969
Sana'a

Ya rasu ranar 15 ga watan Oktoba, 1969, a wani hatsarin jirgin sama a Uzebba, kimanin mil 50 arewa maso yammacin Benin.[2]Yana da shekaru 32 kuma shi kaɗai ne a cikin jirgi a yayin hatsarin. Bayan kwana biyu, a Legas, an yi jana'izar shi a cikin girmamawa irin ta soja.

An sanar da Emmanuel E Ikwue a matsayin wanda zai maye gurbinsa a ranar 18 ga Disamba, 1969.

Manazarta

gyara sashe