Lawal Haruna
Wing Kwamandan (mai ritaya) Lawal Ningi Haruna ya kasance gwamnan soja a jihar Borno, Najeriya daga watan Agusta shekarar 1998 zuwa watan Mayu shekarata alif 1999 a lokacin mulkin rikon kwarya na Janar Abdulsalami Abubakar, ya mika wa zababben gwamnan farar hula Mala Kachalla a watan Mayun shekarar alif 1999.
Lawal Haruna | |||
---|---|---|---|
ga Augusta, 1998 - Mayu 1999 ← Augustine Aniebo, Mala Kachalla | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 1957 (66/67 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
An nada Kyaftin Haruna a matsayin mai kula da Jihar Borno a watan Agustan shekarar alif 1998. Dole ne ya shawo kan takaddama kan tambayar koyar da Ilimi na Addinin Kirista a makarantun gwamnati, wanda shugabanin musulmai a jihar da galibin Musulmi suka yi adawa da shi. A ranar 3 ga watan Nuwamban shekarata alif 1998, ya ba da sanarwar cewa za a fara koyar da Musulmi da Kirista daban a makarantu tare da isassun ɗaliban Kirista, kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. A ranar 11 ga watan Disamba tarzomar ta biyo bayan kiran da wani Limami ya yi na kai wa Kiristoci hari, tare da asarar dukiya mai yawa amma babu mutuwa. A watan Yuni na shekarar alif 1999, an bukaci Haruna ya yi ritaya, kamar sauran tsoffin masu gudanar da mulki na soja.
A watan Disambar shekarar 2000, Haruna ya yi zargin cewa Lt-General Jeremiah Useni ya shirya kashe Shugaban kasa Janar Sani Abacha, wanda ya mutu a sanadiyyar dalilai a ranan 8 ga watan Yuni shekarata alif 1998.
Nassoshi
gyara sashe