Larry Sanger
Lawrence Mark Sanger (An haife shi ranar goma sha shida 16 ga watan Yuli,a shekara ta alif 1968) a garin Bellevue dake babban birnin Kasar Amurka wato Washington. Ba'amurke ne kuma mai samar da ayyuka a kafar yanar gizo, dashi ne aka samar da manhajar Wikipidiya tare da Jimmy Wales, sannan kuma shine ya kirkiri Citizendium.
Larry Sanger | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Lawrence Mark Sanger |
Haihuwa | Bellevue (en) , 16 ga Yuli, 1968 (56 shekaru) |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Mazauni | Columbus |
Karatu | |
Makaranta |
Reed College (en) jami'an jahar Osuo Service High School (en) |
Matakin karatu | Doctor of Philosophy (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | mai falsafa, blogger (en) , computer scientist (en) da ɗan kasuwa |
Employers |
Bomis (en) jami'an jahar Osuo Nupedia Citizendium (en) |
Muhimman ayyuka |
Wikipedia Citizendium (en) |
IMDb | nm2942095 |
larrysanger.org |
Farkon Rayuwa da Karatu
gyara sasheYa girma a garin Anchorage dake jihar Alaska a Amurka a inda nanne mahaifansa suke, Sanger yana karamin yaro yake shaawan karatun ilimomi daban daban, inda ya samu shaidar karatun digiri daga Jami'ar Reed College a shekara ta 1991 da kuma digirin digirgir ko na uku daga Jami'ar Jihar Ohio a shekarar 2000.
Lerry Sanger yakasance daga cikin ma'aikata a manhajoji daban daban wadanda suke samar da ilimomi a yanar gizo, kuma shine shugaban mai gyara rubuta a Nupedia, a inda yaaamar da tsarin infanta baynai kuma yakasance shugaba mai kula da masu taimako na Wikipedia a sanda aka kafa ta, kuma shi yasamar da mafi yawan dokokin da ake amfani dasu a yanzu a manhajar. Sanger yabar Wikipedia a shekara 2002, sannan tun daga nan yafara sukan manhajar ta wikipedia, inda yake fadin cewa, Duk da cewar Wikipidiya tana inganci amma ta rasa a dogara da ita da wasu abubuwan, saboda rashin girmamawa ga kwararru. A watan octoba shekaran 2006 ne Sanger yafara yin wani manhaja mai kama da Wikipedia inda yasa mata suna Citizendium. A watan Disamba ta shekarar 2017 ne aka sanarda cewa Sanger yazama shugaban yada bayanai na manhajar Everipedia, Sanger yakoyar a Jami'ar jihar Ohio, kuma yayi kokari wurin taimakawa a inganta aikin ilimantarwa na WatchKnowLearn. Kuma ya tsara manhajar karatu na yanar gizo wato Reading Bear. Shafinsa na yanar gizo itace Larry Sanger.org