Jimmy Donal Wales ( /ˈdʒɪmi ˈdoʊnəl ˈweɪlz/) ; (An haife shi ranar 7 ga watan Augustan shekara ta 1966) a garin Huntsville da ke jihar Alabama Ƙasar Amurika, yana zaune a Landon da ke Ƙasar Ingila. ɗan kasuwan Kasar Tarayyar Amurka ne.[1][2] Jimmy Wales da Larry Sanger ne suka ƙirƙirar babbar manhajar Wikipedia a shekara ta 2001. Ya yi karatu a Jami'ar Auburn da Jami'ar Jihar Alabama, Tuscaloosa inda ya samu shaidar digiri na biyu a Jami'ar jihar Indiana, Shahararren Dan kasuwan yanar gizo ne, kuma yana da adadin kuɗi sama da Dala miliyan daya ($1,000,000) a shekara ta 2014.

Simpleicons Interface user-outline.svg Jimmy Wales
Jimmy Wales - August 2019 (cropped).jpg
Murya
non-executive director (en) Fassara

27 ga Janairu, 2016 -
Chair of the Wikimedia Foundation Board of Trustees (en) Fassara

20 ga Yuni, 2003 - 28 Oktoba 2006 - Florence Devouard (en) Fassara
Founder's seat (en) Fassara

Rayuwa
Cikakken suna Jimmy Donal Wales
Haihuwa Huntsville (en) Fassara, 7 ga Augusta, 1966 (56 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Birtaniya
Harshen uwa Turancin Amurka
Ƴan uwa
Abokiyar zama Pamela Green (en) Fassara  (1986 -  1993)
Christine Rohan (en) Fassara  (1997 -  2001)
Kate Garvey  (6 Oktoba 2012 -
Karatu
Makaranta Indiana University Bloomington (en) Fassara
Randolph School (en) Fassara
(1979 - 1983)
Auburn University (en) Fassara
(1983 - 1986)
University of Alabama (en) Fassara
(1986 -
Harsuna Turancin Amurka
Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa, blogger (en) Fassara, entrepreneur (en) Fassara, Wikimedian (en) Fassara, computer scientist (en) Fassara, researcher (en) Fassara, orator (en) Fassara, international forum participant (en) Fassara da Ɗan kasuwa
Employers Bomis (en) Fassara  (1996 -  2004)
Fandom (en) Fassara  (2004 -
Muhimman ayyuka Wikipedia
Kyaututtuka
Wanda ya ja hankalinsa Ayn Rand (en) Fassara da Friedrich Hayek (en) Fassara
Mamba Wikimedia Foundation Board of Trustees (en) Fassara
Wikimedia Foundation
Sunan mahaifi Jimbo
Imani
Addini irreligion (en) Fassara
IMDb nm2467065
jimmywales.com
Jimmy Wales signature.svg
Hoton Jimmy Wales a shekara ta 2016.

Farkon rayuwa da karatuGyara

An haifi Wales a Huntsville, Alabama, da tsakar dare a ranar 7 ga watan Augustan 1966, amma shaidar haihuwarsa na nuna 8 ga watan Auguta.

AikiGyara

ShugabanciGyara

Shi ne shugaban Wikia, Inc. tun daga shekara ta 2004 har zuwa yau, Mazaunin Shugaban Wikimedia Foundation daga shekara ta 2003–2006, Chair emeritus of Wikimedia Foundation daga shekara ta 2006 har zuwa yanzu, shi ya amshi Florence Devouard a matsayin shugaban Wikimedia Foundation, Babban Dan kungiyar wikimedia Foundation Creative Commons ne, kuma yana daga cikin masu bada shawara a Sunlight Foundation da MIT Center for Collective Intelligence, a Guardian Media Group ya daina bada shawara a watan Afrilun shekaran 2017.

IyaliGyara

Matansa sune;

  • Pamela Green daga shekara ta (1986 zuwa 1993),
  • Christine Rohan (1997–2011), sai
  • Kate Garvey. Wanda tun daga shekara ta 2012 har yanzu suna tare. 'Ya'yansa guda 3 ne mata.

ManazartaGyara

  1. Jimmy Wales [@jimmy_wales] (September 16, 2019). Jimmy Wales [@jimmy_wales] (September 16, 2019). "I just became a UK citizen, quite happy about that. It occurs to me that perhaps a few MPs should actually take the "Life in the UK" test and study the manual!" (Tweet) – via Twitter.
  2. Horovitz, David (January 7, 2011). "Jimmy Wales's benevolent Wikipedia wisdom". The Jerusalem Post. Archived from the original on August 3, 2018. Retrieved December 26, 2017.